text
stringlengths
3
681
LeBron James ya zama dan wasan kwallon Kwando ta Amurka na farko a tarihi da ya zura kwallaye 50
000
idan aka hada da kwallayen da ya ci kafin da kuma lokacin kakar wasanni a daren ranar Talata James ya fara da wani bugu mai kyau da ya zura kwallo da maki 3 a farko zagaye na farko na wasan Los Angeles Lakers da New Orleans Pelicans James ya samu maki 49
999 a daren ranar Lahadi da ta gabata
lokacin da ya ci kwallaye 17 yayin da Lakers suka doke Clippers da ci 108-102 a karo na shida a jere James ya kai maki 50
000 a kakar wasannisa 22
wanda ake alakanta shi da Vince Carter na wanda ya fi taka leda a tarihin gasar NBA Shahararren dan wasan Lakers Kareen Abdul-Jabar
wanda ya buga kakar wasanni 20
shi ne a mataki na biyu a tarihin gasar NBA da maki 44
149 A yau Litinin
kamfanin Apple ya sanarda cewar zai kashe fiye da dala bilyan 500 a Amurka a cikin shekaru 4 masu zuwa tare da daukar ma’aikata 20
000
sanarwar da ake ganin zata yiwa Shugaba Donald Trump dadi wanda ke yiwa kamfanonin Amurka matsin lamba akan su dawowa da kere-kerensu gida “A yau Apple ya bayyana aniyarsa ta kashe kudade mafi girma
ta shirin kashewa da zuba jarin fiye da dala bilyan 500 a Amurka nan da shekaru 4 masu zuwa
” kamar yadda katafaren kamfanin fasahar sadarwar dake da mazauni a yankin “Silicon Valley” ya bayyana a cikin wata sanarwa A cewar shugaban kamfanin Apple Tim Cook: “muna da kwarin gwiwa game da makomar kere-keren Amurka
muna masu alfaharin dorawa akan jarin da muka jima muna juyawa a Amurka da wannan aniya ta zuba dala bilyan 500 domin dorewar makomar kasarmu.” Haka kuma Apple yace zai dauke ma’aikata kimanin 20
000
wadanda galibi zasu maida hankali akan fannonin bincike da cigaba da fasahar sadarwa da kirkirar sabbin manhajoji da kirkirarriyar basira da kuma koyarwa ta na’ura Sanarwar ta yau Litinin na zuwa ne bayan da Trump yayi shelar aniyar Apple ta zuba jarin bilyoyin daloli a Amurka yayin da yake kwarzanta nasarar tsarin harajin daya zo dashi wajen bunkasa tattalin arzikin Amurka Da yammacin jiya Juma’a ne Majalisar dattawan Amurka ta amince da kudirin kashe kudin gwamnatin
lamarin da ya dakile rufe wani bangaren gwamnatin kana ya shawo kan adawar Democrat ga matakin Majalisar wakilai mai rinjayin Republican ta amince da kudirin tun farkon wannan mako domin cimma wa’adin dake karewa cikin daren ranar Juma’a ta yanda gwamnatin zata ci gaba da gudana 'Yan Democrats a majalisar dattijai sun yi sabani da juna kan ko za su goyi bayan kudurin ci gaba da gudanar da gwamnati na gajeren lokaci
wanda zai ba gwamnatin damar kashe kudade na watanni shida masu zuwa
kana ya rage yawan kudaden da gwamnati ta kashe da kusan dala biliyan 7 a shekarar da ta gabata
da karkatar da kudade ga sojoji da kuma nesantar kashe kudaden da ba na tsaro ba Yawancin 'yan jam'iyyar Democrat sun bayyana fushinsu bayan da jagoran Democrat a zauren majalisar
shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai Chuck Schumer
ya ba da sanarwar a daren ranar Alhamis cewa duk da bai amince da kudirin ba
matakin rufewa zai kasance "zabi mafi muni." Da yake magana a zauren majalisar dattijai da safiyar Juma’a
Schumer ya ce rashin tabbatar da kudirin kashe kudaden gwamnati na Republican zai ba da karin iko ga hukumar DOGE mai kokarin inganta Ma’aikatun Gwamnati da Elon Musk ke jagoranta
ciki har da rufe wasu hukumomi Majalisar dattawan Amurka ta tabbatar da wani kasafin kudin da za akasha don gudanar da ayyukan gwanati da daren jiya Jumma’a
wanda ya kawar da yiwuwar rufe ofisoshin gwamnati na wuciun gadi sannan yayi nasara akan hammayar ‘yan Democrats akan wannan batu An tabbatar da Kudurin dokar bayan da kuri’u aka kada kuri'a 54-46 wanda ya kawar da wani kalubale na tsarin da zai dakatar da mahawara akan matakin wanda ake bukatar akkala kuri’u 60 Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Jumma’a
tsohuwar shugabar majalaisar dattawan Nancy Pelosi
ta ce “Amurka ta shiga irin wannan yanayi inda aka rufe ofisoshin gwamnati a wa’adin Trump na farko
amma babu abinda wannan dokar mai illa zata yi illa ta dada dagula al’amura.” Trump ya bukaci majalisar ta amince da kudirin kasafin kudin sannan jiya Jumma’a ya yaba ma Schumer akan yadda ya bada goyon bayan shi ga kudirin Hadin gwiwa tsakanin masu shirya fina-finai na Isira’ila da Falasdinu ya biyo bayan hatsarin da dan gwagwarmaya Basel Adra ya fada ciki yayin da aka kama shi saboda yunkurinsa na tattara labarin baranar da sojojin Isra’ila ke yi wa garinsa da ke kudu da Yammacin Kogin Jordan
wanda dakarun Isira’ilan ke son amfani da shi a matsayin wurin horar da sojoji Neman gafara da Adra ya yi ba a saurare shi ba har sai da ya yi abota da wani dan jarida Bayahuden Isira’ila wanda ya taimaka masa wurin bada labarin sa “Mun yi wannan fin ne a matsayin mu na Falasdinawa da Isira’ilawa
saboda idan muka hada kai
muryoyin mu sun fi karfi
” in ji dan jarida kuma mai shirya fina-finai Yuval Abraham Ya yi amfani da jawabin amincewarsa wajen yin kira ga gwamnatin kasarsa kan abin da ya kira “mummunar lalata Gaza da al’ummarta.” Kuma ya yi kira ga Hamas da ta saki dukkan ‘yan Isira’ila da take garkuwa da su Shirin “No Other Land” ya kasance a cikin jerin shirye shiryen da suka kayatar a daren
bayan nasarar yin fice a bukin fina-finan A bukin kyautar Oscar
ya doke “Porcelain War
” “Sugarcane
” “Black Box Diaries” da kuma “Soundtrack to a Coup d’Etat.” An dauki shirin ne tsawon shekara hudu tsakanin 2019 zuwa 2023
inda aka kammala aikin kwanaki kafin Hamas ta kaddamar da mummunar harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kan Isira’ila da ya janyo aka fara yakin Gaza A cikin fim din
Abraham ya shiga cikin fadan al’umma da raba mutane da muhallan su
amma ya fuskanci turjiya daga Falasdinawan da ke nuna alfarmarsa a matsayinsa na dan Isira’ila Adra ya ce ya kasa barin Yammacin Kogin Jordan kuma ana daukarsa kamar mai laifi
yayin da Abraham yake shigowa yana fita ba tare da tsangwama ba Hannayen jari sun kara yin asara a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Wall Street a ranar Talata yayin da yakin kasuwanci tsakanin Amurka da manyan abokanan kasuwancinta ya karu
inda kasuwar S&P 500 ta rasa dukkan ribar da ta samu tun ranar zabe Gwamnatin Trump ta Sanya haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Canada da Mexico da ya fara aiki a ranar Talata da kuma rubanya karin haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga China Dukkan kasashen uku sun dauki matakan rama shirin saka haraji
lamarin da ya janyo damuwa kan tafiyar hawainiya na tattalin arzikin duniya Kasuwar S&P 500 ta fadi da kashi 1.2 cikin 100 yayin da sama da kashi 80 cikin 100 na hannayen jarin da aka rufe ya yi kasa Kasuwar Dow Jones ta yi kasa da kashi 1.6 cikin 100 Manyan kamfanonin fasaha sun dan fadi da kashi 10 cikin 100 daga mafi girman rufewarta na baya bayan nan
wanda shi ne abin da kasuwa ke la’akari da gyara
amma Nvidia
Microsoft da sauran manyan kamfanonin fasaha sun samu bunkasa inda suka taimaka wajen daidaita wadannan asarar Manajar Microsoft mai kula da kasashen Najeriya da Ghana
Ola Williams
ce ta sanarda hakan yayin rangadin duba kirkirarriyar basirar da kamfanin yayi a jihar legas a yau laraba “Ina mai farin cikin sanarda cewar mu a matsayinmu na kamfanin Microsoft dake Najeriya
zamu zuba jarin dala milyan guda nan da shekaru 2 masu zuwa domin baiwa ‘yan Najeriya milyan 1 horo akan dabarun sarrafa kirkirarriyar basira
” kamar yadda Williams ta sanar cikin shauki Ta kara da cewar da wannan horo
matasan najeriya zasu samawa kawunansu hanyar samun kudin shiga mai dorewa tare da yin gogayya da takwarorinsu a matakin duniya Rangadin kirkirarriyar basirar na Microsoft ya tattauna a kan makomar fasahar da kuma irin damammakin da za ta samar a fannonin rayuwa daban-daban Real Madrid ta doke Atletico Madrid a bugun fenariti a gasar Zakarun Turai ta Champions League don ci gaba da kare kambunta a ranar Laraba tare da samun tikitin shiga wasan quarter-final Dan wasan baya Antonio Rüdiger ne ya zura bugun fenariti na karshe wanda ya tabbatar da nasarar 4-2 bayan ‘yan wasan Atletico biyu sun kasa cin nasu Atletico ta yi nasarar 1-0 bayan mintuna 90 a filinta na Metropolitano
wanda ya kawar da rinjayen Madrid na 2-1 daga wasan farko Tauraron Madrid
Vinícius Júnior
ya buga fenariti da ta tashi saman ragar Atletico Dan wasan Atletico
Conor Gallagher
ne ya fara jefa kwallo tun farkon wasan Ayyanawar na kunshe ne a cikin jaridar rundunar ‘yan sandan da aka wallafa a daren jiya Litinin
wacce kakakin rundunar ta jihar Ogun
Omolola Odutola ya yada A cewarta
harin ya faru ne a ranar 5 ga watan Febrairun 2025
da misalin karfe 10 na safe sa’ilin da jami’an shiyar Ota na ma’aikatar tsara birane ta jihar Ogun; Onabanjo Abidemi da Raymond Lateef da Ridwan Oyero Akinlesi ke tsaka da gudanar da aikinsu na tursasa bin dokar gine-gine a yankunan Oke-Osa da Tigbo Ilu Ota Mijin shahararriyar mawakiyar salon wakar country Dolly Parton
Carl Thomas Dean
ya mutu yana da shekaru 82 Parton ce ta yada labarin mutuwar a sanarwar data wallafa a shafukanta na sada zumunta a jiya Litinin "Ni da Carl mun shafe dimbin shekaru masu dadi a tare
" kamar yadda ta wallafa "kalamai ba za su yi adalci ba wajen bayyana irin kaunar da ke tsakaninmu tsawon fiye da shekaru 60 Ba'a bayyana musabbabin mutuwarsa ba
duk da cewarsakon da ta wallafa ya bayyana cewa ya mutu ne a garin Nashville na jihar Tennessee
inda ma'uratan ke zaune A cewar sakon da Dolly Parton ta wallafa a shafinta na sada zumunta a jiya Litinin
za'a birne Dean a wani kebebban bikin da danginsa na kusa zasu halarta Wani mutumin kasar Austireliya da ake yabawa saboda ceton rayuwar jarirai fiye da milyan 2 ta hanyar shafe shekaru yana bada gudunmowar jini ya mutu yana da shekaru 88 James Harrison wanda jininsa ke dauke da wani nau'in sinadarin protein da ba kasafai ake samunsa ba dake baiwa jiki kariya
ya mutu ne a cikin baccinsa a ranar 17 ga Febrairun daya gabata a wani asibitin Austireliya da ke jihar New South Wales
a cewar kungiyar bada agaji ta Red Cross da ake kira da lifeblood Harrison ya ba da gudunmowar jini sau 1
173
a cikin fiye da shekaru 60 bai taba saba alkawarin daukar jinin da aka yi dashi ba har sa'ar da ya yi ritaya a shekarar 2018 yana da shekaru 81 A 1999
an bashi babbar lambar girmamawa ta kasar Austireliya da nufin yabawa irin talafawar da yake baiwa lifeblood da kuma shirin hada alluran anti-d Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM) da tauraron tawagar kwallon kafar Super Eagles Ahmad Musa sun bukaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya fado daga wani gini ya mutu a kasar Uganda A jiya Litinin aka bada rahoton mutuwa Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce dan wasan haifaffen Sokoto ya mutu ne bayan daya fado daga benen wani kaafaren kanti Sa’o’i bayan faruwar lamarin mai ban takaici
shugabar hukumar nidcom
Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewar akwai “ababen zargi” game da mutuwar Lawal @ahmad musa718 da @nidcom_gov za su tabbatar kuma suna bukatar a gudanar da cikakken bincike a bayyane
Allah ya jikansa tare da baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi kamar yadda ta wallafa a shafinta na X da maraicen yau Talata @nidcom_gov za ta tabbatar kuma tan a bukatar a gudanar da cikakken bincike a bayyane
Allah ya jikansa tare da baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.” Kwallon da James Tarkowski ya farkewa Everton ana daf da busa tashi a gasar da aka tashi kunnen doki ci 2-2 a ranar 12 ga watan Fabrairun da muke ciki ce ta haddasa hatsaniyar Alkalin wasa ya kori Arne Slot da mataimakinsa Sipke Hulshof tare da Curtis Jones na Liverpool da dan wasan tsakiyar Everton Abdoulaye Doucoure daga filin Hukumar kwallon kafar Ingila (FA) ta fitar da sanarwa a yau Laraba tana cewa wata hukumar ladabtarwa mai zaman kanta ta hukunta kungiyoyin kwallon kafar Everton da Liverpool da kuma Slot da Hulshoff Geir Pedersen ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a
ranar da ake cika shekaru 14 da fara zanga-zangar neman demokradiyya wadda ta kai fiye da shekaru goma ana yakin basasa "Abin da ya fara a matsayin neman sake yin garambawul a harkokin mulkin kasar
ya gamu da mummunan zalunci
wanda ya haifar da daya daga cikin rikice-rikice mafyai muni a tarihin wannan zamanin
" in ji Pederson Iyalai na ci gaba da nuna alhinin rashin 'yan uwansu
al'ummomi na ci gaba da wargajewa
miliyoyin mutane sun bar gidajensu
kuma da yawa suna ci gaba da neman wadanda suka bata." Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya raba mutane kusan miliyan 12 da muhallansu a Syria
ciki har da 'yan gudun hijira sama da miliyan 6 An hambarar da gwamnatin Assad ne a watan Disamban 2024
amma kazamin tashin hankali da aka fara a ranar 6 ga watan Maris a yankin gabar tekun Syria da ya janyo asarar rayuka
ya dakushe fatan samun kwanciyar hankali
inda jami’an tsaro suka yi artabu da mayakan da ke biyayya ga tsohon shugaban
wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane
ciki har da fararen hula da dama