text
stringlengths 20
374
|
---|
Sai dai masanin ya kara da cewa: ''Abin shi ne mun san cewa Isra'ila tana da shirin nukiliya, mun san tana da bama-bamai, kuma mun san tana iya amfani da su.'' |
Jaridar Israel Hayom, wadda ake bayarwa kyauta kuma mai goyon bayan Netanyahu, ta rubuta wata makala mai tsawon gaske a kan karfin nukiliya na Iran |
Jaridar ta nuna cewa, ''babbar manufar Isra'ila ita ce hana bazuwar makaman nukiliya ta ko yaya.'' |
Kuma masu goyon bayan manufar barin shirin a dukunkune, suna ganin yin watsi da wannan manufa, ka iya janyo gasar mallakar nukiliyar a Gabas ta Tsakiya - wanda hakan zai kawo gasar makamai |
Bayani na farko da ya taba fitowa fili a kan karfin nukiliya na Isra'ila ya samu ne daga wata takardar ma'aikatar harkokin waje ta Amurka 1962, kan maganar wata yarjejeniya tsakanin Faransa da Isra'ila da ta kai ga ginatashar samar da lantarki ta nukiliya a birnin Dimona na kudancin Isra'ila a shekarun 1950 |
Bincike ta taswirar Google ya nuna wannan cibiya ta nukliya - Negev, an gina ta ne a wani yanki mai nisan kilomita goma kudu da birnin Dimoma, a tsakiyar saharar Negev |
Da farko dai an bayyana cibiyar a matsayin masaƙa da cibiyar nazari kan karafa da kuma ayyukan gona |
Bayan nan kuma a cikin shekarun 1960, tsohon firaministan Isra'ila David Ben-Gurion, a karon farko ya yi nuni kan shirin nukiliya na Isra'ila |
A wani jawabi da ya yi ga majalisar dokokin Isra'ila (Knesset), ya sanar da cewa cibiyar binciken ta nukiliya ta ayyukan zaman lafiya ce |
Bohigas ya ce rahotanni da bincike da ma'aikatar tsaro ta Amurka da makamashi, sun nuna ƙarara cewa Isra'ila tana da makaman nukiliya |
Takardun sirri waɗanda daga baya aka bayyana su ga jama'a sun nuna cewa aƙalla daga shekarar 1975, Amurka tana da tabbacin cewa Isra'ila ta mallaki makaman nukiliya |
To amma kuma a duk waɗannan bayanai babu wanda a tarihi ya tona asirin shirin nukiliya na Isra'ila kamar tonon-sililin da tsohon ma'aikacin nukiliya na Isra'ila Mordechai Vanunu ya yi |
Vanunu tsohon injiniya ne a cibiyar nukiliya ta Dimona, inda ya yi aiki tsawon shekara tara |
Kafin ya bar aikin a 1985, a ɓoye ya ɗauki hotuna na cibiyar |
Waɗannan hotuna sun nuna kayayyakin haɗa makaman nukiliya da ma ɗakin bincike na haɗa makaman |
A 1986, Vanunu ya haɗu da 'yan ƙungiyar yaƙi da makaman nukiliya a birnin Sydney, Australia, inda ya haɗu Oscar Guerrero, tsohon ɗanjarida na Colombia, wanda ya shawo kansa ya wallafa waɗannan hotuna da ya ɗauka cikin sirri |
Daga nan ne, Vanunu ya tuntuɓi Peter Hunnam, na jaridar Birtaniya ta Sunday Times |
Daga nan aka gurfanar da shi a gaban shari'a inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara18 a gidan sarka bisa laifin cin amanar ƙasa da leƙen asiri don bayyana sirrin nukiliyar Isra'ila |
Bayan an sake shi a 2004, ya bayyana cewa yana alfahari da farin cikin abin da ya yi |
An kuma sake kama shi aka gurfanar da shi a gaban kotu a kan saɓa dokokin da aka gindaya masa |
Tun daga wannan lokacin an hana shi mu'amulla da 'yan ƙasashen waje ko kuma ya fita daga Isra'ila |
Bayan tonon-sililin da Mordechai Vanunu, ya yi, daga nan ta tabbata cewa Isra'ila tana da makaman nukiliya |
Kamar yadda bayanan da aka wallafa a jarida, waɗanda Mordechai Vanunu, ya fitar, ƙwararrun sun yi ƙiyasin cewa Isra'ilatana da makaman nukiliya tsakanin 100 zuwa 200 |
A yau kuma wasu cibiyoyin nazari irin su cibiyar binciken zaman lafiya ta Stockholm, suna ƙiyasin cewa Isra'ila tana da makaman nukiliya wajen 90 |
A yanayin da ita Isra'ila a hukumance ba ta bayar da wasu bayanai ba a kan shirin nata na makaman nukiliya, to ta yayya za a iya lissafa yawan makana da take da |
''A duk shekara hukumomin duniya na sa ido a kan shirye-shiryen nukiliya na ƙasashe daga na kuma su fitar da bayanai,'' in ji Buhigas |
"To amma ga ƙasashen da babu bayanai a kansu – kamar Isra'ila da Koriya ta Arewa, ana amfani da ƙiyasin yawan sinadarin yureniyom ko fulutoniyon da suka fitar a shekarar da ta gabata, daga nan ne za a iya ƙiyasin abin da ƙasar ke da shi,'' in ji masanin |
A 2012, Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya zartar da wani ƙuduri wanda ya yi kira ga Isra'ila kan ta buɗe ƙofa ga hukumomin duniya su shiga su daba ayyukanta na nukliya |
To amma kuma Isra'ilar da Amurka da ma Kanada suka ƙi amincewa da wannan ƙuduri, wanda kuma ya yi kira ga Isra'ila ta shiga yarjejeniyar hana bazuwar makaman nukiliya |
Sau da dama kuma har yanzu Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, na gabatar da ƙudurin, zaman yankin Gabas ta Tsakiya wanda babu makaman nukiliya a cikinsa |
Shi kuwa Javier Buhigas ya nuna cewa: "Abin damuwa ne a ce wata ƙasa ta mallaki makaman nukiliya, saboda mallakar waɗannan makamai babban haɗari ne." |
''Kasancewar Isra'ila wadda a kullum take saɓa ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da kawara da kai daga dokokin duniya da dokokin jin-ƙai na duniya, tana da makaman nukiliya, kuma ba wata ƙasa da za ta hana ta, wannan ne ma ya ƙara sa zaman lamarin babban abin damuwa.'' |
Liverpool ta bi sahun Manchester United da Arsenal a zawarcin ɗanwasan Sporting mai shekara 27 Viktor Gyokeres |
(Correio da Manha - in Portuguese) |
Chelsea ta kusa ƙulla kwantiragi da ɗanwasan Borussia Dortmund da Ingila ɗan ƙasa da 21 Jamie Gittens mai shekara 20, yayin da ƙungiyar ta Bundesliga ke fatan samun shi kan fam miliyan 50 |
Manchester United na iya amincewa da tayin fam miliyan 45 don ta samu cefanar da ɗanwasan Argentina mai shekara 20 Alejandro Garnacho |
Newcastle na ƙyalla ido kan ƴanwasa irin su Johan Bakayoko mai shekara 23 da ke buga wa PSV Eindhoven da Belgium da ɗanwasan Borussia Dortmund da Jamus, Kerim Adeyemi mai shekara 23 idan haƙarsu ba ta cimma ruwa ba a ƙoƙarinsu na ɗauko ɗanwasan Nottingham Forest da Sweden Anthony Elanga mai shekara 23 |
Manchester United na fuskantar ƙalubalen sayar da ɗanwasan Netherlands Tyrell Malacia mai shekaa 25 wanda ya taimaka wa PSV Eindhoven lashe kofin Eredivisie yayin da yake zaman aro a kakar da ta wuce |
Sunderland ta tattauna da Nice kan yarjejeniyar da ta shafi golan Poland mai shekara 25, Marcin Bulka |
Everton ta soma tattaunawa da Villareal na La Liga kan ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan gaba na Faransa mai shekara 22 Thierno Bary kuma ba su yanke ƙauna da biyan fam miliyan 34 ba na tanadin kwantiragin |
Manchester United ta yi watsi da tayin fam miliyan 6.5 daga Hoffenheim kan ɗanwasan Ingila ɗan ƙasa da shekara 21 Callum Doyle |
Everton na ci gaba da fatan sayen ɗanwasa Kenny Tete duk da rahotanni da ke cewa Fulham ta yi wa mai shekara 29 ɗin ɗan asalin Netherlands tayin sabunta kwantiraginsa |
Har yanzu Benfica ba ta samu tayi daga Real Madrid ba bayan da aka alaƙanta kulob ɗin da neman Alvaro Carreras mai shekara 22, wanda a bara, daga Manchester United ya koma Lisbon |
Al'ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu baƙin ƴanbindiga sun tarwatsa ƙauyuka da dama a yankin |
Ɗanmajalisar jiha da ke wakiltar yankin ya ce wasu baƙin ɓarayi ne daga kasashen waje suke kaddamar da sababbin hare-haren a sassan yankunan kananan hukumomin Bukkuyum da Anka na jihar Zamfara |
Faru Nasarawa Burƙullu, mai wakiltar Bukkuyum ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara ya ce ƴanbindigar sun kashe sama da mutum 20 |
Ya ce al'amarin ya kai maƙura, har yana neman hana gudanar da harkokin noma a daminar bana a yankunan da abin ya shafa |
Ya ce al'ummar yankin musamman Ruwan Rana da Bukkuyum ta arewa suna cikin tashin hankali kuma mutane da dama ne ke gudun hijira |
"Ƴanta'addan sun zo da yawa sun kashe mutane sun kuma kwashi shanu da raƙuma da awakai," in ji shi |
Ɗanmajalisar ya yi iƙirarin cewa kusan kashi 70 na mazaɓun da yake wakilta suna ƙarƙashin ikon ƴanbindigar |
Ya ce lamarin ya fi ƙamari a yankin Adabka da Kairu da Kyaram da Gwashi da ƙauyukan Ruwan Rana da Ruwan Jema da Gasa Hula Ƙurfar Danya da Barayar Zaki da Rafin Gero, duka babu zaman lafiya |
"Ƴanta'adda su ne hakimai, kuma su suke yin hukunci," in ji shi |
Ɗanmajalisar jihar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha su kawo masu ɗauki domin yaƙar ƴanbindigar don al'umma su samu su yi noma |
Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammaci da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu fashin daji |
Ƴanbindigar suna kai farmaki ƙauyuka, su kashe, su saci mutane tare da kone gidaje bayan sun wawushe kayan mutane |
Wasu jiga-jigan 'yan hamayya a Najeriya, ƙarƙashin inuwar ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG), na ƙoƙarin tabbatar da wata haɗaka mai ƙarfi da nufin kawar da gwamnatin APC ƙarƙashin Bola Tinubu |
Tun a farkon shekarar nan ne ƴan mahayyar suka fara tunanin kafa wata haɗaka domin cimma wannan ƙudiri nasu |
Ƴan hamayyar sun samar da wata ƙungiyar haɗaƙa da aka yi wa suna ''All Democratic Alliance'' (ADA), wadda suka aike wa hukumar zaɓen ƙasar da nufin yi mata rajista don zama jam'iyyar siyasa |
Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa a ranar 20 ga Yunin |
Ƙawancen haɗakar na ƙunshe da jiga-jigan hamayya a fagen siyasar ƙasar, da suka fito daga ɓangarorin ƙasar daban-daban daga mabambantan addinai |
Wannan ne ma dalilin da ya sa wasu ke ganin haɗakar za ta yi ƙarfi, kasancewar tana da wakilci a sassan daban-daban na ƙasar |
Ƴansiyasa ne da a baya suka riƙe manyan muƙamai a baya, kuma har yanzu suke da tasiri a fagen siyasar ƙasar |
Manyan jiga-jigan da ake gani cikin wannan sabuwar tafiya sun haɗa da: |
Jagoran adawar ƙasar a baya ya sha yin takarar shugaban ƙasa, kuma a 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu ƙuri'a kusan miliyan bakwai |
Atiku wanda a yanzu ɗan jam'iyyar PDP ne ya kasance jigo a siyasar Najeriya, tun lokacin da ya zama mataimakin shugaban ƙasa a 1999 zuwa 2007 |
Ɗan siyasar - wanda Bafulatani ne daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya -ana yi masa kallon ɗaya daga cikin mafiya tasiri a fagen siyasar Najeriya |
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar na daga cikin fitattun mutanen da suka ƙulla haɗakar da ta haifar da jam'iyyar APC a 2014, da ta yi nasarar ƙwace mulki a hannun PDP a 2015 |
A yanzu dai jam'iyyar PDP na da gwamnoni 10 a faɗin Najeriya, kuma kodayake babu gwamnan da ya bayyana bin Atiku zuwa sabuwar haɗakar, ana ganin ficewar tasa za ta sa wasu gwamnonin su bi shi |
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar LP, na daga cikin mutane na gaba-gaba a kafa sabuwar tafiyar ta ADA |
Peter Obi - wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne har sau takwas - ya kasance na uku a zaɓen shugaban ƙasar da ta gabata a 2023, inda ya samu ƙuri'a fiye da miliyan shida |
Mista Obi - wanda ɗan ƙabilar Igbo ne daga kudu maso gabashin Najeriya - na da farin jini musamman tsakanin ƴanƙabilarsa |
Lamarin da ya sa jam'iyyarsa ta LP ta samu nasara a jihohi 12, ciki har da Legas da da Abuja a zaɓen shugaban ƙasar na 2023 |
Jam'iyyarsa ta LP na da gwamnan guda a jihar Abia, kuma ana ganin wataƙila ya bi shi cikin sabuwar haɗakar |
A watan Maris da ya gabata ne El-Rufai ya bayyana ficewa daga jam'iyyar APC tare da komawa SDP |
Nasir El-Rufai ya kasance ministan Abuja tsakanin 2003 zuwa 2007, kafin ya zama gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar, har wa'adi biyu tsakanin 2015 zuwa 2023 |
A kakar zaɓen 2023, fitaccen ɗan siyasar - wanda Bahaushe ne - ya kasance na gaba-gaba wajen goyon bayan Bola Tinubu na APC |
To sai dai bayan lashe zaɓen Tinubu ɓaraka ta kunno kai tsakaninsa da El-Rufai bayan da majalisar dattawa ta ƙi amincewa da tantance shi domin ba shi muƙamin minista a gwamnatin |
Ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers mai arzikin mai fetur da ke yankin kudu maso kudancin ƙasar daga 2007 zuwa 2015 |
Bayan kammala wa'adinsa a matsayin gwamnan jihar Rivers, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa shi ministan sufuri na tsawon shekara takwas daga 2015 zuwa 2023 |
A 2022 ya bayyani anisarya ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, to amma ya sha kaye a hannun Tinubu a zaɓen fitar da gwani |
Rauf Aregbesola ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, har tsawon wa'adi biyu daga 2010 zuwa 2018 |
A shekarar 2019 tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa shi, muƙamin ministan harkokin cikin, muƙamin da ya riƙe har 2023 |
Aregbesola Bayarabe ne da ya fito daga yankin kudu maso yammacin Najeriya |
A farkon shekarar nan ne Rauf Aregbesola ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC |
David Mark ɗan asalin jihar Benue - wanda tsohon jami'in soji ne- ya taɓa zama gwamnan mulkin soji na jihar Neja daga 1984 zuwa 1986 |
Ya kuma riƙe muƙamin ministan sadarwa kafin ya zama ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Benue ta Kudu |
Shi ne shugaban majalisar dattawa mafi jimawa a muƙamin, bayan jagorantar majalisar na tsawon wa'adi biyu (shekara takwas) daga 2007 zuwa 2015 |
Ya kasance ɗan ƙabilar Idoma daga yankin arewa ta tsakiyar Najeriya |
Sun yi tafiyar dubban kilomitoci kan sirdi domin bin wata daɗaɗɗiyar hanyar ƙasa da Musulman Andalus suka riƙa amfani da ita shekaru 500 da suka gabata domin zuwa aikin Hajji |
Mutanen sun yi tafiyar sama da wata bakwai kafin isa ƙasar Saudiyya |
Hikayata gasa ce ta rubutun ƙagaggun gajerun labarai ta mata zalla wadda ke samar da dama ga mata zalla marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa |
Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo |
Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa |
Gasar dai ta mata zalla ce waɗanda shekarunsu ba su gaza 18 ba sannan kuma ba su wuce 35 ba ya zuwa ranar 17 ga watan Agustan 2025 |
Za a rufe gasar ne da ƙarfe 11:59 agogon GMT na ranar 17 ga watan Agustan 2025 |
Ba za a yi maraba da duk labarin da aka aiko bayan rufe gasar ba |
Akwai tukwicin kuɗi da lambar karramawa da za a bai wa gwarazan gasar |
Dole ne a aiko da labaran ta ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin biyu: |
Ta hanyar cike wannan fom ɗin da ke ƙasa : |
Ka da a manta cewa dole ne mai shiga gasar ta zama mai shekara tsakanin 18 zuwa 35 sannan kuma wannan gasa ce ta mata zalla |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.