text
stringlengths 20
374
|
---|
Kuma irin wannan yanayi yakan shafi fannonin fasaha da ƙere-ƙere da ke nan doron duniya, har ma yana haddasa katsewar lantarki, amma ba ya da illa kai tsaye ga lafiyar ɗan'adam |
Samun haɗari a duniyar rana ba baƙon al'amari ba ne |
Yana faruwa ne a yayin da rana ke fitar da tururinta da ke tashi kamar wuta kuma wanda ke ɗauke da sinadarai daban-daban masu watsuwa a sararin samaniya |
Tururin mai ɗauke da sinadaran lantarki kan yi tafiya mai nisa cikin ƙanƙanin lokaci kamar walkiya, domin yakan ɗauki tsawon mintuna takwas ne kacal ya iso duniyar bil’adama |
Ƙarfin tururin da rana ke fitarwa yana fitar da hasken wuta mai launi daban-daban |
Hukumar NASA ta ce tururin rana yana da tasiri ga ɓangaren sadarwar rediyo da hasken lantarki da kuma yadda ake aikewa da saƙonni ta intanet |
A shekarar 2017, an samu manyan-manyan tururin rana guda biyu da suka haddasa cikas ga na'urorin da ke gano wurare irin su GPS |
Yayin da a watan Febrairun 2011 kuma an samu wani tururin rana mai ƙarfin gaske da ya kawo cikas ga sadarwar rediyo a ƙasar Chana |
A can shekarun baya a shekarar 1989 ma an samu wani tururin rana da ya haddasa ɗaukewar lantarki wadda ta jefa miliyoyin mazauna lardin Quebec na ƙasar Canada a cikin duhu har na tsawon sa'a 9 |
Yayin da a shaekarar 1859 wani tururin shi ma da ya auku a lokacin ya haifar da wani hadarin da ya shafi bangaren sufurin jiragen ƙasa na Victoria |
Wannan lamari ne da har yanzu ana iya samun sa kuma yana da matuƙar haɗari, kamar yadda wani bincike ya nuna |
Jami'ar Lanchester da ke Birtaniya ta gargaɗi hukumar da ke lura da sufuri jiragen ƙasar da ta shirya wa aukuwar hadarin da ke ɗauke da tururin rana da zai iya haifar da tangarɗa duk kuwa da cewa ba a cika samun irin haka na faruwa ba |
Rana dai an halicce ta ne da wasu nau'in iskar gas mai motsi, wada ke samar da ƙarfin fizgar magaɗishu |
Ƙarfin fizgar kan rinƙa juyawa, abin da ake kira juyawar rana |
Wannan kan haifar da sararin jikin na rana ya yi tumbuɗin da zai iya kawo hadarin tururin ranar |
Duk bayan shekara 11 ko fiye ƙarfin fizgar maganaɗisu da ke kudanci da arewacin jikin ranar kan riƙa yi yana sauyawa daga wannan wuri zuwa wancan |
A cewar ƙungiyar ƙwararru waɗanda suka haɗa da na hukumar Nasa da Hukumar da ke lura da yanayin teku ta Amurka (NOAA), sun ce yanayin na yanzu da ke jujjuyawa da ake kira Solar Cycle 25, ya soma ne a watan Disamban 2019 |
Nasa da NOOA sun ce a yanzu rana ta riga ta kai ƙolin lokacin wannan jujjuyawa ta rana a bara |
A daidai ɓangarorin waɗannan baƙaƙen sassan da ke cikin rana akan samu fashewa mai ƙarfi, waɗanda kan yi duhu sosai kasancewar sun yi sanyi fiye da zagayensa |
Galibin su sun mamaye sararin da ya kai girman duniyar ƙasa ta ɗan'adam ko ma fiye |
Hadarin da ke haifar da tururin rana da kan kai ƙolinsa a duk bayan shekara 11 da takan kammala zagayawa |
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wani abu da ya tsunduma ƙasarsa cikin rikicin da ke tsakanin Iran da Isra'ila bayan ya ƙaddamar da hare-hare kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran |
Wannan wani abu ne da ya ƙare dagula lamurra game da yaƙin wanda ake ganin zai sanya ƙasashe su dauki ɓangare, ko dai ta suka ko kuma goyon bayan Isra'ila da kuma abin da Amurkar ta yi |
Gabanin harin da Amurka ta kai cikin Iran, wato bayan hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamar kan Iran a ranar 13 ga watan Yuni, babu wata ƙasa da ta fito ta ce za ta taimaka wa ɗaya daga cikin ɓangarorin da kayan yaki kai-tsaye |
Sai dai, wasu daga cikin martanin da aka samu daga ƙasashen duniya bayan bama-baman da Amurka ta jefa a Iran ya yi nuni ga barazanar da ta taso na ƙazancewar rikicin tsakanin ƙasashen duniya |
Sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana a shafinsa na X cewa "ya kaɗu matuƙa da matakin da Amurka ta ɗauka na amfani da ƙarfi kan Iran." Sannan ya ƙara da cewa "harin na Amurka na barazana ga zaman lafiya a duniya baki ɗaya |
"Akwai barazanar wannan yaƙin zai yaɗu zuwa wasu sassan duniya, har ma ya wuce tunanin mutane tare da jefa fararen hula cikin bala'i," in ji shi |
A ƙarshen mkon jiya, ministocin harkokin wajen ƙasashen turai sun gana da takwaransu na Iran, domin jin ra'ayinsa kan yiwuwar shiga sabuwar yarjejeniyar nukiliya |
Sai dai ita Iran ta sake nanata cewa ba za ta shiga wata tattaunawa ba har sai Ira'ila ta daina kai mata hare-hare |
Jim kaɗan bayan harin na Amurka ne ƙasashe da dama suka fara bayyana rashin jin daɗinsu, inda wasu ma suka fito suka bayyana goyon baya ga Iran |
Bayan harin, Iraq ta fito ta yi Allah-wadai da matakin, sannan ta yi gargaɗin hakan zai iya jawo raɗuwar yaƙin, wanda zai iya ƙara hargitsa nahiyar |
Tun da farko, Iraq ta nuna goyon bayanta ga Iran ne bayan hare-haren Isra'ila a ranar 13 ga Yuni a lokacin taron kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta fito ta soki matakin na Isra'ila |
Ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce harin Amurka a cibiyar nukiliyar Iran ya ƙara ta'azzara fargabar yaɗuwar yaƙin, sannan ya bayyana fargabar abin da zai iya biyo baya |
Sai dai a jawabin ministan - wanda wataƙila ke nuna matsayar ƙasar a matsayin mai sulhunta tsakanin ƙasashen nahiyar - ya ƙi amfani da kalmar "Allah-wadai." |
Sai dai jawabinsa ya yi hannun riga da na shugaban ƙasar, inda Recep Tayyip Erdoğan wanda ya ce Iran na kare kanta daga haramtaccen yaƙi ne |
Ya kuma nanata cewa Iran na da haƙƙin kuma doka ta amince da haka |
Pakistan, wadda ƙawar Amurka ce, kuma ƙasar Musulmi ɗaya tilo da aka san tana da makamin nukiliya, ta ce harin Amurka ya saɓa "dokokin duniya." |
Ministan harkokin wajen Pakistan ya ƙara da cewa Iran "na da haƙƙin kare kanta a ƙa'idar Majalisar Ɗinkin Duniya." |
Kafin harin na Amurka, Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Ishaq Dar ya ce, "babu wanda ya san inda yaƙin nan zai tsaya ba." |
Awanni bayan harin Amurka a Iran, Jordan ta tare wasu makamai masu linzami da suka biyo sararin samaniyarta domin zuwa Isra'ila |
Amma Sarkin Jordan Abdullah ya yi gargaɗi a wani jawabi da ya gabatar a gaban zauren majalisar turai cewa, "harin a Iran na barazana ga yankin da ma duniya baki ɗaya." |
Gwamnatin Taliban ba ta ce komai ba game da harin na Amurka, amma a baya ta sha nuna goyon bayanta ga Iran |
Kamar yadda wasu rahotanni suka nuna, ministan harkokin wajen Afghanistan ya bayyana wa takwaransa na Iran cewa hare-haren Isra'ila sun "saɓa da dokokin duniya da ƙa'idar Majalisar Ɗinkin Duniya." |
Saudiyya - wadda ɗaya ce daga cikin ƙawayen Amurka mafiya muhimmanci a Gabas ta Tsakiya, inda kuma sansanonin sojin Amurka da dama suke - ta fito cikin sauri ta yi Allah-wadai da harin na Amurka, inda ta buƙaci a dakata da rikicin baki ɗaya |
Duk da cewa Saudiyya da Iran ba sa ga maciji, ƙasashen biyu sun shiga wata yarjejeniyar gyara tsakaninsu wadda China ta jagoranta a watan Maris na 2023 |
Haka ita ma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - wadda ita ma ƙawar Amurka ce - ta ce harin na Amurka zai ƙara tsananta rashin zaman lafiya a yankin da ma duniya baki ɗayanta |
Oman - wadda ta kasance kan gaba wajen shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran ta yi Allah-wadai da harin, sannan ta bayyana "fargabarta" kan abin da zai biyo bayan harin |
A nata ɓangaren Qatar ta ce tana sa ido kan abubuwan da ke faruwa |
A ƙasar akwai ɗaya daga cikin manyan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya |
Shugaban Ƙasar Lebanon, Joseph Aoun ya bayyana takaicinsa, inda ya bayyana a wata sanarwa cewa "kai hari a cibiyar nukiliyar Iran ya ƙara jawo fargabar tsaro a nahiyar." |
Amma ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, da ke Lebanon, wadda ta shiga yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a bara, ta bayyana a wani rahoto ta jaridar The Times of Israel ta kalato cewa ba za ta kai hari a Isra'ila ko sansanonin Amurka a yankin ba domin mayar da martani kan harin Amurka |
Ƙungiyar Houthi da ke Yemen wadda ke samun goyon bayan Iran ta yi Allah-wadai da harin, sannan ta nuna goyon bayanta ga Iran, inda ta yi barazanar kai hari kan jiragen ruwan Amurka |
Azerbaijan ta nuna takaicinta kan harin, sannan ta yi kira da a fahimci juna, duk da cewa ƙasar na da alaƙar soji da Isra'ila |
Zuwa yanzu dai Syria ba ta ce komai ba a hukumance game da harin na Amurka a Iran |
Ƙasashen Turai dama can sun fi nuna goyon bayan Isra'ila da Amurka game da fargabar mallakar nukiliyar Iran, amma suna fargabar ƙazancewar yaƙin a duniya |
Bayan harin na Amurka, wani babban jakada a tarayyar turai, Kaja Kallas ya yi kira da a koma teburin sulhu |
Ƙasashen turai da dama sun sha bayyana goyon bayansu ga Isra'ila kan kai hari a Iran |
A baya, shugaban Jamus, Friedrich Merz ya yi maraba da yunƙurin Isra'ila na kai hari a Iran |
Ofishin Shugaban Faransa Emanuel Macron ya ce shugaban ya tattauna da Saudiyya da Oman a ranar Lahadi |
Faransa na kira ne da a samu sasanci, tare da "gujewa duk wani matakin da zai jawo ƙazancewar yaƙin," kamar yadda ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya wallafa a shafin X |
Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya nanata matakin tarayyar turai ne, sannan shi ma ya yi kira da koma teburin sulhu, a daidai lokacin da yake bayyana fargabarsa kan yunƙurin Iran na mallakar makamin nukiliya |
"Ba zai taɓa yiwuwa ba Iran ta mallaki makamin nukiliya, kuma Amurka ta ɗauki matakin magance wannan matsalar," in ji Starmer a shafin X, sannan ya ƙara da cewa, "zaman lafiya a yankin shi ne ya fi muhimmanci." |
Amma babban ɗan jam'iyyar Labour, Emily Thornberry, ya bayyana matakin da Trump ya ɗauka na kai harin a matsayin "kuskure babba |
Kafin harin na Amurka, ministan harkokin wajen Australia Penny Wong ya ce Isra'ila na da haƙƙin kare kanta |
Tun da farko, Canada ta soki matakin Iran na kai hari a Isra'ila |
Ministan harkokin wajen ƙasar, Anita Anand, ta ce tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu ne ya fi muhimmanci |
Rasha ta ce harin Amurka na nuna "yaƙin ya fara faɗaɗa" amma China da fi ɗaura laifi kan Isra'ila, inda ta ce ya kamata "ta dakata da hare-hare ba tare da ɓata lokaci." |
Rasha da China duk sun sha bayyana goyon bayansu ga Iran, tare da sukar Isra'ila |
A ƴan shekarun nan dai an ga yadda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniya tare da zama ƙawayen Iran na ƙud da ƙud |
Da farko, China da Rasha sun fara ɗaukar mataki ne mai sauƙi, amma da rikicin ya fara ƙamari, sai suka fara shiga lamarin dumu-dumu |
Kafin harin Amurka, China ta gargaɗi Washington kan kai hari a Iran |
Ita kuma India, ta yi gum ne an lamarin, wanda ba zai rasa nasaba ba da yunƙurinta na gyara alaƙar soji da Isra'ila |
Barcelona na tunanin ɗaukar aron ɗan wasan gaban Manchester United ɗan ƙasar Ingila Marcus Rashford mai shekara 27 |
Ɗan wasan Liverpool da Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, ya fi bayar da fifiko kan komawa Napoli idan har ya bar Anfield a bazarar nan |
Nottingham Forest ta yi watsi da tayin da Newcastle ta yi mata na kusan fam miliyan 45 kan ɗan wasan Sweden Anthony Elanga, mai shekara 23, wanda ta ƙaƙaba masa farashin Fam miliyan 60 |
Chelsea na fatan gaggauta kammala cinikin ɗan wasan gaban Borussia Dortmund ɗan ƙasar Ingila Jamie Gittens, yayin da Bayern Munich ma ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 20 |
Newcastle na da niyyar mayar da ɗan wasan gaban Sweden Alexander Isak mai shekara 25 ya zama ɗan wasan da ya fi samun albashi mafi tsoka a tarihin kulob ɗin don kawar da zawarcin da Liverpool da Barcelona da kuma Arsenal |
Fenerbahce na zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 25, wanda farashinsa ya kai Fam miliyan 25 |
Sunderland ta tuntuɓi Sassuolo game da yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Faransa Armand Lauriente mai shekara 26 |
Everton da Manchester United na zawarcin ɗan wasan Leicester ɗan Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 28, wanda zai iya barin ƙungiyar a kan farashin fam miliyan 9 |
Har yanzu Leeds ba ta samu tayi kan golan Faransa mai shekara 25 Illan Meslier ba duk da rahotannin da ke cewa yana shirin zuwa gwada lafiyarsa a Fenerbahce |
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao ɗan ƙasar Sifaniya Nico Williams, mai shekara 22, wanda ke da farashin fam miliyan 50 a kwantiraginsa, ya shaidawa ƙungiyar cewa yana da sha'awar komawa Barcelona |
Burnley na shirin gabatar da tayin fam miliyan 12 kan ɗan wasan Lazio ɗan kasar Faransa Loum Tchaouna, mai shekara 21 |
A ranar Litinin ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran, wanda ya ce zai kai ga samar da dawwamammen zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu |
Hakan ya zo ne bayan kwashe kwana 12 ana musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu, tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hari na farko a ranar 13 ga watan Yuni |
Matakin da Amurka ta ɗauka na jefa bama-bamai a cibiyoyin nukiliyar Iran ya ƙara ruruta barazanar da aka shiga na fargabar yaɗuwar rikici a faɗin Gabas ta Tsakiya |
Tuni yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara tangal-tangal, inda shugaban Amurka Donald Trump ya zargi dukkanin ɓangarorin biyu da karya yarjejeniyar |
Idan yarjejeniyar ta yi nasara, ana sa ran za ta taimaka wajen cimma zaman lafiya mai ɗorewa |
Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wata ma'ana ɗaya tilo ta 'tsagaita wuta' duk da cewa kalmar ta samo asali ne daga kalaman sojoji na "cease fire" (tsagaita wuta), wadda akasi ce ta "open fire" wato buɗe wuta |
Ya danganta da abin da ɓangarorin biyu masu faɗa da juna suka amince a kai |
Tsagaita wuta abu ne da ya ƙunshi samar da wata yarjejeniya a hukumance wadda ta ƙunshi: |
Haka nan yarjejeniyar za ta iya bayyana ayyukan soji da za a iya yi da kuma waɗanda aka haramta, da kuma yadda za a sanya ido kan aiki da yarjejeniyar |
Zai ta iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan |
Wani lokaci ɓangarorin da ke adawa da juna za su iya amincewa kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi ko kuma tsagaita wuta kafin gudanar da wani abu = |
Akan yi hakan ne domin rage tsananin rikicin ko kuma domin kai agaji |
Akan iya ƙulla ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta domin samar da yanayin da zai bayar da damar tattaunawa domin neman samun matsaya kan zaman lafiya na dindindin |
Majalisar Dinkin Duniya ta taɓa shirya yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo ƙarshen yaƙin basasa a Lebanon a shekarun 1978 da 1981 da kuma 1982 |
Sai dai yaƙin ya riƙa ci gaba a duk lokacin da yarjejeniyar ta ƙare, kuma ba a samu damar kawo ƙarshen rikicin ba har sai a shekara 1990 |
Isra'ila da Hamas sun kira tsagaita wuta da aka ƙulla tsakaninsu a Nuwamban 2023 a matsayin ta kai agaji |
Tsagaita wuta domin kai agaji a wasu lokuta ana amfani da su domin rage tsananin yaƙi ko kuma domin rage uƙubar da al'umma ke ciki |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.