text
stringlengths
20
374
Misali, gwamnatin Sudan ta taɓa cimma yarjejeniya da ƙungiyoyin ƴan tawaye biyu, wato Ƙungiyar ƴanta al'ummar Sudan (SLM) da ta tabbatar da adalci da daidaito (JEM), lamarin da ya sa aka tsagaita wuta na kwana 45 domin bai wa ƙungiyoyin agaji damar kai kayan agaji ga al'umma
A 2004, bayan ambaliyar Tsunami ta fada wa ƙasar Indonesia, gwamnatin ƙasar da kuma ƙungiyar Free Aceh Movement sun ayyana tsagaita wuta domin bayar da damar kai agaji a yankunan da ake yaƙi
Akwai kuma yarjejeniyar da akan ƙulla domin kawo ƙarshen yaƙi a wani takamaiman yanki
A shekarar 2018, Majalisar Dinkin Duniya ta cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Yemen da ƴan tawayen Houthi domin daina yaƙi a yankin tashar ruwa ta Hodeida domin kare al'ummar yankin
Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata
Haɗin gwiwar jami'an sa-kai a jihar Zamfara sun yi wa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan mai ƙaurin suna, Bello Turji ƙofar rago a wata maɓoyarsa tare da gwabza ƙazamin faɗa
Hukumomin jihar sun ce jami'an sa-kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Bello Turji fiye da 100 a farkon wannan mako
Sun ƙaddamar da harin ne da gudunmawar wani tubabben ɗan bindiga, Bashari Maniya wanda ya jagoranci kai farmakin a kusa da ƙauyen Cida na ƙaramar hukumar Shinkafi
Mataimaki na musamman kan harkokin tsaro ga Gwamnan Zamfara, Alhaji Ahmad Manga ya ce "an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya"
'Yan sa-kan CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji
Majiyoyi sun ce an kuma kashe jami'an sa-kai da wani soja sannan da Bashari Maniya
Wani ɗan jarida mai bibiyar rikicin 'yan fashin daji a Arewa maso Yamma ya ce daga bayanan da ya samu, an yi wa motarsu Bashir Maniya kwanton ɓauna ne, inda aka kashe shi tare da wasu jami'an JTF uku
Wannan dai kusan shi ne karon farko a cewar gwamnatin jihar Zamfara, da jami'an tsaron da ta samar suka samu nasarar kai farmakin har maɓoyar babban ɗan fashin daji
Bello Turji riƙaƙƙen jagoran 'yan fashin daji ne da ya dade yana addabar sassan jihar Zamfara da sauran maƙwabtan jihohi
Hukumomin Najeriya sun kwashe tsawon shekaru suna nemansa ruwa a jallo kuma a baya-bayan nan sun daɗa ƙaimi a ƙoƙarin kama shi musamman bayan kashe wasu manyan 'yan fashin daji irinsa kamar Halilu Sububu da Manore da Damuna
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami'an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne
"Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi" in ji Ahmad Manga
Ya ƙara da cewa "an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka kashi mutanensa, wanda shi kansa bai iya ƙididdige abin da ya rasa, sai dai daga baya"
Ya ce duk inda ka ga gawawwaki to akasari na yaransa ne
Mataimaki na musamman kan sha'anin tsaron ya ce Bashari Maniya ya gamu da ajalinsa ne sakamakon hatsarin da motarsu ta yi lokacin da ta faɗa wani rami
"Sabuwar mota ce wanda ba duk mutum ya san kanta ba, sun taka wani rami ne mai kama da rijiya kuma suna a guje, motar ta ƙwace kuma ta je ta faɗi
Ba wai shi ne ya yi nasarar buge motar ba, a'a."
Ya ƙara da cewa lokacin da aka kai musu ɗauki an samu Maniya da sauran waɗanda ke cikin motar ne ba a hayyacinsu ba, saboda motar harbi ba ya ratsa ta
Alhaji Ahmad Manga ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Zamfara za ta ci gaba da farautar Bello Turji ba rdare ba rana
"Wallahi sai abin da ya ci gaba
Duk ɗan jihar Zamfara zai gaya maka musamman ɗan yankin Shinkafi sun sani, abin da aka yi shekara 14 yana gallaza wa mutane
Shi ya san rawar da jami'an tsaro suka taka yanzu ba a taɓa isko shi ba, irin yadda aka tarad da shi har gidansa
Ya bayyana aniyar gwamnatin Zamfara na shigo da ƙarin dakarun sojoji don ci gaba da tunkarar Bello Turji
A cewarsa, ko a faɗan da aka yi ranar Litinin Bello Turji laɓewa ya riƙa yi, kafin daga bisani ya arce
Shi dai Mannir Fura Girke, ɗan jarida mai bibiyar rikicin 'yan fashin daji Mannir Fura Girke ya ce a iya saninsa Bashir Maniya, 'yan'uwan Kachalla Dull ne wanda su Bello Turji suka kashe a 2022 amma ya tuba tare da ɗan'uwansa Kabiru Maniya inda suke taimaka wa jami'an tsaro
Ya ce faɗan yaƙi ne na sunƙuru tsakanin jami'an tsaron Najeriya da kuma su kansu 'yan fashin daji
Bayanai dai sun tabbatar da cewa an kai harin karkashin jagorancin Bashari Maniya, wanda tsohon dan bindiga ne da ya taba kai hare-hare a yankunan a can baya kafin ya tuba, inda suka aukawa sansanin Bello Turjin har ma ta kai da dama daga mayakansa suka rasa rayukansu
Wasu rahotanni dai sun ce kafin kai wannan harin, ɗan bindigar Bello Turji ya samu labarin hakan, inda ya tattara mayaƙa da yawansu ya kai dubu daya domin tunkarar jami'an tsaron
Luguden wutar bamabamai da Amurka ta yi a kan tashoshin nukuliya na Iran ba su lalata makamashin nata ba, a cewar wani bincken farko-farko da hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi
Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana rahoton da aka kwarmata wa manema labarai da "cikakkiyar ƙarya" da wani "ƙaramin ma'aikaci a ɓangaren tattara bayanan sirri ya fitar"
Shugaba Trump ya sake nanata cewa hare-haren sun lalata tashoshin nukilyar "gaba ɗaya" kuma ya zargi kafofin yaɗa labarai da "yunƙurin ƙasƙantar da ɗaya daga cikin hare-hare mafiya nasara a tarihi"
Amurka ta kai wa tashoshin uku hare-hare da suka ƙunshi Fordo, da Natanz, da Isfahan ta hanyar jefa musu bamabaman da ke iya ragargaza ramukan da ke ƙarƙashin ƙasa masu zurfin mita ƙafa 60 na kankare ko kuma ƙafa 200 na ƙasa
Sai dai majiyoyin da ke da masaniya kan bayanan sirrin na Amurka sun ce akasarin na'urorin sarrafa makamashin da ake kira centrifuges "lafiyarsu ƙalau" kuma iya saman ginin kawai aka lalata - ban da ramukan ƙarƙashin ƙasar
An toshe wasu hanyoyin shiga tashoshin biyu, kuma an lalata wasu daga cikin kayayyakin, amma akasarin wurin da ke can ƙarƙashin ƙasa ba su ji komai ba
Bayanan da ba a bayyana wanda ya kwarmata su ba sun ce abin da kawai hare-haren suka cimma shi ne rage wa Iran sauri "na 'yan watanni", kuma saurin ma zai danganta ne kan irin gaggawar da Iran ɗin ta yi na lalubo abubuwan da aka binne a ƙarƙashin ƙasar saboda harin
Wasu majiyoyin sun kuma tabbatar wa CBS cewa Iran ta kwashe wasu daga cikin makamashin uranium da ta sarrafa tun kafin a kai mata hare-haren
An yi ta tunanin cewa makeken bam ɗin Amurka ) Massive Ordnance Penetrator mai nauyin kilogiram 14,000, shi ne kaɗai ne zai iya tarwatsa masana'antar samar da nukiliyar ta Iran da ke ƙarƙashin ƙasa
Iran ta sha nanata cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne ba don yaƙi ba
'Yan awanni bayan kai harin na ranar Asabar, shugaban majalisar rundunonin tsaron Amurka Janar Dan Caine ya faɗa wa manema labarai cewa za a ɗauki lokaci kafin tabbatar da abin da ya faru a wurin harin
Amma ya nanata cewa "duka tashoshin uku an tarwatsa su sosai"
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna ramuka shida sababbi a kusa da mashigar ramuka biyu na Fordo, da ƙura da kuma ɓaraguzai
Ba za a iya tabbatar da komai ba daga hotunan, ballantana kuma irin ɓarnar da bama-baman suka yi a ƙarƙashin ƙasar
Hassan Abedini, mataimakin shugaban sashen siyasa na kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran ya ce na kwashe kayayyaki daga tashoshin uku "babu daɗewa" kuma Iran "ba ta yi wata asara mai yawa ba saboda tuni aka kwashe kayan."
A gefe guda kuma, jami'an gwamnatin Amurka na ta yabon nasarar hare-haren kamar takwarorinsu na Isra'ila
Cikin wata sanarwa a ranar Talata, Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce "bisa ga abubuwan da muka gani – kuma na ga komai da komai – hare-harenmu sun tarwatsa ikon Iran na ƙera makaman nukiliya"
"Duk wanda y ace bama-baman ba su yi aiki da kyau ba kawai yana so ne ya yi wa shugaban ƙasa zagon ƙasa da kuma nasarar aikin," in ji Hegseth
"Idan suka ce sun tarwatsa Shirin na Iran, ba su bayyana ko suna nufin lalata na'urorin centripuges da kuma damar ci gaba da sarrafa uranium nan gaba, ko kuma suna nufin tarwatsa makamashi da aka riga aka samar," a cewar Sherman
"Dukkan abubuwa, ciki har da kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa Vance, na nuna cewa ba mu tarwatsa sarrafaffen makamashin ba," in ji shi
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya faɗa ranar Talata cewa suns amu nasarar daƙile yunƙurin Iran ɗin na samun nukiliya tun bayan fara kai wa juna hare-hare ranar 13 ga watan Yuni, ciki har da lalata makamanta masu linzami
"Mun kawar da barazana biyu daga kanmu – barazanar harin nukiliya da kuma ta makamai masu linzami 20,000 na Iran," a cewar Netanyahu cikin wani saƙon bidiyo
Wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Saudiyya Al Hadath ta wallafa ya Ambato wata majiya daga Isra'ila na cewa sun yi imanin an binne mafi yawan makamashin da Iran ta riga sarrafa a ƙarƙashin ɓaraguzai
Amurka na da hukumomin leƙen asiri 18, waɗanda a wasu lokutan ke fitar da rahotonni masu cin karo da juna bisa ga fahimtarsu da kuma ɓangaren da suke lura da shi
Misali, har yanzu hukumomin sun kasa cimma matsaya kan inda cutar Korona ta samo asali
Akwai yiwuwar a samu wasu bayanan nan gaba da za su bayar da ƙarin masaniya kan al'amarin
A ranar Litinin Iran ta kai harin ramuwa kan sansanin Amurka na Al-Udeid da ke Qatar
An kakkaɓe akasarin makaman kuma babu wanda ya ji Rauni
Tun bayan ramuwar ta Iran, an samutsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran wadda har yanzu take aiki
Jim kaɗan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin Iran da Isra'ila, jiniyar ankararwa ce ta tayar da mazauna birnin Beersheba daga barci tun da farar safiya a ranar Talata saboda makaman Iran da suka sauka
An rubuta cikin saƙonnin gargaɗi da aka tura wa mazauna yankin ta waya cewa "babbar ankararwa"
Sai kuma daga baya jiniya ta fara ƙara
Kamar saura, Merav Manay da iyalanta sun tsere zuwa ɗakin tsira - wani ɓanagare na gidan nasu da aka gina da kankare ninki biyu da kuma ƙofar ƙarfe mai nauyi domin samun kariya daga harin roka
Lokacin da makamin na Iran ya auka, sun ji gidan ya girgiza kuma babu abin da suka yi sai ɗora hannaye a ka
"Ƙarar ta yi ƙarfi da yawa har mun zaci ƙarshenmu ne ya zo," in ji ta
Bayan sun fito, sun tarar da tagogi duka sun ɗaiɗaice saboda girman fashewar
Merav ta ci gaba da zama a ginin tsawon wasu awanni cikin firgici da rashin tabbas na abin da za ta gani a wajen ginin
A tsallaken titi kuma, wani gini ne mai kama da nasu ya ragargaje saboda makamin ya faɗa kan sa kai-tsaye
Bayan harin, likitoci da sojojin Isra'ila sun ruga zuwa Baeersheba domin ceto mutane
Jim kaɗan bayan harin na Baeersheba ne Isra'ila da Iran suka tabbatar cewa sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta, sai kuma suka fara zargin juna da karya ta
Yayin da mazauna Baeersheba ke alhinin wannan hari da ya lalata garinsu, sun kuma nuna damuwa kan ko yarjejeniyar za ta ɗore
Da yammacin Talata, Oren Cohen mai shekara 45 ya tsaya kan ɓaraguzan gidansa da ke kallon gidan da makamin ya faɗawa
Ya ce ba zai iya ma kallon ginin ba
"Ina cikin damuwa game da 'ya'yana, sai yanzu ma na lura da abin da ya faru a nan," a cewarsa
Oren na tare da matarsa da 'ya'yansa uku – masu shekara takwas, 12, da 15 – lokacin da aka kai harin, inda ya ce tagar ɗakin mai nauyi ta wangale saboda tsananin ƙarar harin
Duk da yadda lamarin ya shafe shi kai-tsaye, Oren ya ce yana goyon bayan yaƙin da Isra'ila ke yi da Iran a lokacin
"Ina ganin ba mu da zaɓi," in ji shi
"Mun yi abin da ya zama dole ne domin kare kanmu."
Ya ce bai sani ba ko zai "iya dogara" da tsagaita wutar amma ya ce ya yarda da gwamnatin Isra'ila za ta iya tantancewa ko ta cimma duka buƙatunta a Iran
Lokaci na farko da Merav ta fita domin duba abin da ya rage na unguwar tasu a ranar Talata, ita ma ta ce tana da tabbas Isra'ila ba ta da wani zaɓi ne illa ta ka iwa Iran hari
"Da ma dole ne wannan ta faru ko yanzu ko nan gaba
Mun shirya tsaf," kamar yadda ta bayyana
Donald Trump, shugaban da ya sake komawa Fadar Gwamnatin Amurka (White House ) a watan Janairu da alƙawarin zama mai wanzar da zaman lafiya, abin mamaki ya jefa ƙasarsa cikin yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila
Saɓanin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da ya sake komawa kan mulki, Trump a yanzu na jagorantar yankin da ke dab da rincaɓewa da yaƙi fiye da, a baya - yaƙin da ita kanta Amurka ke da hannu dumu-dumu a ciki
A wani jawabi da ya yi ga al'ummar ƙasar daga Fadar Gwamnatin (White House), sa'a biyu bayan da ya sanar a shafinsa na intanet cewa sojojin Amurka sun kai hari kan cibiyoyin nukiliya uku a Iran, shugaban na Amurka ya ce, an yi gagarumar nasara a harin
Shugaban ya bayyana fatan cewa matakin nasa zai bayar da damar samun dawwamammen zaman lafiya- inda Iran ba ta da sauran wani ƙarfi ko dama ta zama mai makamin nukiliya
Sai dai kuma a nata ɓangaren Iran ta ce wannan hari da Amurka ta kai mata illa ƴar kaɗan ya yi wa tashar ta nukiliya ta Fordo mai tsananin tsaro
A yanzu dai ba wanda ya san gaskiyar lamarin - sai dai kamar yadda ƴan magana kan ce lokaci alƙali - nan gaba gaskiyar lamarin za ta bayyana
Trump wanda yake kewaye hagu da dama da manyan ƙusoshin gwamnatinsa - Mataimakin Shugaban Ƙasa JD Vance, da Sakataren harkokin waje Marco Rubio, da kuma Sakataren harkokin tsaro Pete Hegseth, ya gargaɗi Iran cewa idan ba ta yi watsi da shirinta na nukiliya ba, za ta fuskanci wasu munanan hare-hare a nan fiye da wanda ta gani a yanzu
Duk da wannan tunƙaho da jijji da kai da fankama da shugaban yake nunawa ci gaba da shiga wannan rikici ta kai hare-hare a Iran zai iya kasancewa wani mummunan abu ga Amurka da yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya yi gargaɗin samun tashe-tashen hankali a dalilin shigar Amurka wannan rikici kai tsaye, yana cewa dama tuni yankin yana dab da faɗawa rikici
Idan Iran ta rama kamar yadda Ayatollah Ali Khamenei ya yi gargaɗin cewa idan Amurka ta kai wa ƙasarsa hari to, hakan kuma zai ƙara sa Amurka ta ƙara martani
Furucin da Trump ya yi a makon nan cewa dole ne Iran ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba, ya tura shugaban inda yake da wuya ya iya dawowa baya
Ita ma Iran da irin barazanar da take yi ta sa nata a irin wannan matsayi
Mai kaya ya rantse ɓarawo ya rantse - yadda husuma a nan za mu ce yaƙi yake farawa ke nan - daga nan kuma sai abin da hali ya yi domin zai yi ta girma har ma ya fi ƙarfin tunani da ikon waɗanda suka janyo shi
A ranar Alhamis, Donald Trump, ya ba wa gwamnatin Iran wa'adin mako biyu kafin ya yanke shawara kan ko ƙasarsa za ta shiga yakin kai tsaye ko kuma a'a, to amma sai ya yi gajen haƙuri, ya ƙosa da kwana biyu kawai
A ranar Asabar da daddare shugaban na Amurka ya sanar da cewa Amurka ta ɗauki mataki