text
stringlengths
20
374
Kun san cewa rikicin Isra'ila da Iran na iya janyo durƙushewar tatalin arziƙin duniya
A ƙarshen makon da ya gabata ne rikici tsakanin Isra'ila da Iran ya yi ƙamari, bayan da Isra'ilar ta fara kai wa Iran ɗin hare-hare, inda ita ma Iran ta mayar da martani kuma abin ya koma kai wa juna hare-haren da ke janyo rashin rayuka da gine-gine
Ku kalli ƙarin bayani a bidiyon da ke sama
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Tun farkon makon ne aka batun tazarcen shugaba Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin mataimaki, lamarin da ya fara jefa jam'iyyar APC cikin ruɗani bayan abin da ya faru a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiyyar arewa maso gabas
An samu ruɗani a taron da shugabannin yankin suka gudanar a ƙarshen mako a jihar Gombe bayan da shugabannin jam'iyyar APC na ƙasa suka ambaci shugaba Tinubu shi kaɗai a matsayin wanda za iyi wa APC Takara a zaɓen 2027 ba tare da ambatar mataimakinsa ba Kashim Shettima
Matakin ya haifar da yamutsi a zauren taron, lamarin da ya sa har ta kai ga ba wa hammata iska a taron wanda ya ƙunshi shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin yankin na jam'iyyar APC da ministoci da tsaffin gwamnoni da jiga-jigan jam'iyyar
Haka kuma a farkon makon an wayi gari da wasu jerin hare-haren ƴanbindiga da suka hallaka mutane da dama a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya
Hukumomi a Najeriya sun ce hare-haren sun halaka fiye da mutum 100, yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki, ana sa ran adadin zai zarta haka
Jihar Benue na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi ƙaurin suna wajen rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya
Hare-haren baya-bayan nan biyu da aka kai ranar 13 da 14 ga watan Yuni sun tayar da hankalin ƴan ƙasar, lamarin da ya sa shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kawo ƙarshen rikicin
A makon ne kuma wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar hukumar Dan Musa ta jihar Katsina sun ajiye makamansu tare da sakin mutum 16 da suka yi garkuwa da su
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ta ce matakin na cikin wani shiri na ci gaba da karɓar makamai da ficewa daga harkar aikata laifuka wanda rundunar Operation Fasan Yamma ke jagoranta tare da hadin gwiwar hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki
Jagororin 'yan bindigar da suka miƙa wuya sun haɗa da Kamulu Buzaru da Manore da Nagwaggo da Lalbi da Alhaji Sani da Dogo Baidu da Dogo Nahalle da Abdulkadir Black
Haka kuma a cikin makon ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, yana mai jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam'iyyar PDP
A wata sanarwa da tsohon mai taimaka masa a harkar yaɗa labarai, Umar Sani, ya fitar, Namadi Sambo ya bayyana jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya mai cike da ruɗani da kuma wata don ɓatar da jama'a
Sanarwar ta bayyana cewa hoton da ke yawo da ya tayar da wannan jita-jitar wanda ke nuna Sambo tare da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tsohon hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce a lokacin da gwamnan ya kai masa ziyara ta jaje a gidansa da ke Abuja, bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo
"Wasu na ƙoƙarin amfani da hoton domin yaudarar jama'a da ƙirƙirar labarin da bai da tushe ne kawai." Sanarwar ta ƙara da cewa
A makon ne kuma dai wata kotu a Abuja ta bayar da belin Sanata Natasha kan naira miliyan 50 tare da ɗaga shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Satumba
Gwamnatin Najeriya ce ta shigar da ƙarar Sanata Natasha bisa zarge-zarge uku da suka ƙunshi zargin ɓata sunan shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanat Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
Haka kuma a cikin makon mayaƙan ƙungiyar nan ta Lakurawa sun gargaɗi al'ummomin garuruwa fiye da goma na yankin ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi, a kan su yi watsi da dabarar sayar da shanun huɗa suna sayen wasu na'urorin zamani na huɗa da ke amfani da man fetur
Mayakan sun ce za su halaka duk wanda ya ki jin gargadin nasu
Manoman dai kan sayar da shanun su sayi na'urorin huda saboda tsoron da suke yi, cewa 'yan bindigar suna sace musu dabbobi
Kashedin da ake zargin 'yan kungiyar ta Lakurawa sun yi wa jama'ar garuruwan, ya jefa fargaba da zaman dar-dar ga mutanen yankin
Haka kuma daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankali a makon akwai ziyarar da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kai a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar
Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Sanat Uba Sani ya aiwata tsawon shekara biyu da ya shafe yana mulkin jihar
Cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da wani asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya
Haka kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana'o'i, sai kuma motocin safa masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100
A ranar Juma'ar makon ce kuma jagororin jam'iyyun hamayya na Najeriya a ƙarƙashin inuwar gamayyar jam'iyyun hamayya ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam'iyyar da za su yi amfani da ita domin fafatawa da jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa
Tuni NNCG ta miƙa takardar neman rajistar jam'iyya ga Hukumar INEC a hukumance
Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar 20 ga Yunin
A wasiƙar, sun rubuta cewa, "muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance ta zama jam'iyyar siyasa."
Daina ganin waƙoƙi da raye-raye a finafinan Hausa sun fara jan hankali masu kallo, inda wasu suke fargabar ko dai an daina saka waƙoƙin ne, lamarin da masana suke ganin ci gaba ne mai kyau ga masana'antar
Tun farkon finafinan Kannywood, masana'antar ta yi fice wajen amfani da waƙa a matsayin wani muhimmin jigo na labari
Ana dai amfani da waƙoƙin ne ko don nuna soyayya, ko nuna baƙin ciki, ko kuma don ƙarfafa wani saƙo, wanda bai rasa nasaba da kamanceceniyar da finafinan Hausa ke da shi da finafinan Indiya
Sai dai a wani sabon yanayi, yawancin sabbin finafinai ko dai babu waƙa, ko kuma an yi amfani da waƙar ne kawai domin sharar fage
Yanzu finafinan Kannywood da suka fi dace, masu dogon zango ne, kuma finafinai ne da ake daɗewa ana yi, ba kamar yadda ake yi finafinai masu gajerin zango na wasu awanni ba
A game da abin da ya sa aka rage sanya waƙoƙi a finafinan, Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne ta Jamus, wanda ya yi fice wajen sharhi kan harkokin finafinai, musamman Kannywood, ya ce ƴan masana'antar ne suka fi dacewa su bayar da amsa
Sai dai ya ce tun asali dama, "amma dai tun asali da aka fara waƙa, ba ta samu karɓuwa ba sosai, ba kowa ba ne ya karɓe ta
Wasu suna sakawa amma a bayan fage, ba tare da an fito ana rawa da waƙa ba," in ji shi
Ya ƙara da cewa, "A ɓangaren nazari, muna ganin mutane da dama ba za su damu ba don an daina saka waƙa a fim domin dama akwai ƙorafi cewa rawa da waƙa ba al'adar Hausawa ba ce - duk da cewa wasu na ganin al'adun fim daban, al'adar mutane daban."
A nasa ɓangaren, Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru Ɗan Hajiya wanda mai shirya finafinai ne a Kannywood, ya ce yanayin lokaci ne da kuma sauye-sauyen da aka samu a harkar
"Yanayin labaran finafinan ne suka canja, yanzu an koma masu dogon zango
Sai ya zama finafinai masu dogon zangon an fi buƙatar samar da labari mai kyau da zai ɗauki hankalin mutane ya ja su."
Ɗan Hajiya ya ƙara da cewa ba su cika mayar da hankali kan waƙa ba kamar yadda aka saba a finafinan masu gajeran zango, "waɗanda zuwa ɗaya za ka kalla na awa ɗaya ko ɗaya da rabi
Don haka ne aka ratsa waƙoƙi domin nishaɗantar da mai kallo mai
Wannan kuma kallo za a yi na watanni
Wannan shi ne babban dalilin rabuwa da waƙoƙi."
Sai dai wannan rage ganin waƙoƙin a finafinan ya haifar da muhawara a tsakanin masu bibiyar masana'antar, inda wasu suke ganin ci gaba ne mai kyau, wasu kuma suke ganin yana da kyau a riƙa abin da Hausawa suke kira da "taɓa kiɗi, taɓa karatu." wato a riƙ jefa waƙoƙin
A game da wannan, Dokta Muhsin ya ce, "Ni dai a nawa ra'ayin, rage sanya waƙa a fim ci gaba ne saboda dama wasu lokuta ana saka waƙoƙin ba a wuraren da ba su dace ba
Za ka ga an saka a waƙa a wuraren da babu dalilin yin waƙar
Ko da ake yin waƙoƙin, akwai masu yin masu ma'ana, akwai waɗanda ba su da ma'ana
Su cigaba da waƙoƙinsu
Don haka su cigaba da waƙoƙinsu, mawaƙa ma su cigaba da waƙoƙinsu," in ji shi
A game da makomar mawaƙan Hausa, Dokta Muhsin Ibrahim ya ce ba dole sai an yi waƙoƙi a cikin finafinai ne za a tabbatar da mafita ga mawaƙan na Hausa
Ya ce, "A ɓangaren mawaƙa, ai yanzu suna yin waƙoƙinsu
Akwai shirin fitattun mawaƙa na Arewa24, za ka ga suna nuna waƙoƙin suna fita, sannan ga Youtube, sannan kuma ga Sportify
Ya ƙara da cewa baya ga waɗannan hanyoyin, "ana gayyatarsu bukukuwa, sannan suna yi wa ƴansiyasa waƙoƙi da sauransu
Don haka ba sai sun yi waƙa a fim ba ne za su samu tagomashi."
Shi ma Naziru Dan Hajiya ya ce an fara amfani da waƙoƙin wajen tallata finafina masu dogon zango, saboda a cewarsa akwai masu sha'awar waƙoƙi, "kuma ana amfani da su wajen tallata finafinan."
A game da ko za a dawo da sanya waƙoƙi a finafina nan gaba, Naziru ya ce, "Akwai wasu suna sanya waƙoƙi domin tallata finafinansu
Ke nan an fara da dawo da waƙoƙin, amma ba a cikin fim ɗin
Don haka za a yi amfani da waƙa domin tallata fim ɗin, ko da kuwa ba a saka a cikin fim ɗin ba."