Dataset Viewer
Auto-converted to Parquet
text
stringlengths
20
374
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna sabbin alamomi na ɓarna a titunan shiga da hanyoyin ƙaƙashin ƙasa na tashar sarrafa nukiliyar Iran da ke ƙarƙashin tsaunuka a Fordo
Ranar 23 ga watan Yuni ne Isra'ila ta kai wa cibiyar hari, kwana guda bayan Amurka ta saki bama-bamai masu tarwatsa ginin ƙarƙashin ƙasa a wurin
Ɓarnar da ba na gani ba a baya ta kuma bayyana a kusa da mashigar cibiyar ƙarƙashin ƙasa ta Tashar Fasahar Nukiliyar Isfahan bayan Amurka ta kai mata hari
Haka kuma akwai alamomi da ke yadda ake ta aiki don cike ramukan da hare-haren Amurka suka yi a cibiyar sarrafa yuraniyam ta Natanz
Wasu bayanan leƙen asiri na Amurka da aka tsegunta sun bayyana tantama a kan ko hare-haren sun cimma burin ruguza cibiyoyin nukiliyar Iran na ƙarƙashin ƙasa
Rahotannin kafofin yaɗa labarai a kan hakan sun fusata Shugaba Donald Trump wanda ya mai da martani cikin ɓacin rai
Sauran sabbin hotunan tauraron ɗan'adam sun bayyana ɓarnar da ba a gani ba a baya a wata jami'a da ke arewa maso gabashin Iran da kuma a wani yanki kusa da wani babban filin jirgin sama yamma da birnin Tehran
Isra'ila da kuma daga bisani Amurka sun ce hare-haren na da nufin hana Iran ƙera makamin nukiliya
Iran dai ta sha musanta waɗannan zarge-zarge, inda ta dage cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne
Cibiyar sarrafa nukiliyar Fordo, da ke binne a ƙarƙashin tsaunuka a kusa da birnin Ƙum, an jefa mata bama-baman lalata gine-ginen ƙarƙashin ƙasa na Amurka ranar 22 ga watan Yuni, abin da ya haifar da manyan ramuka guda shida da ake iya gani a hotunan tauraron ɗan'adam, baya ga diddigar ƙura da ɓaraguzan da suka watsu a faɗin yankin
Bayan kwana guda kuma, Isra'ila ta ce ta sake kai hari Fordo, inda a wannan lokaci ta far wa titunan shiga cibiyar
Hukumomin Iran daga bisani sun tabbatar da harin
Hotunan tauraron ɗan'adam masu fitar da komai sarai da aka ɗauka ranar 24 ga watan Yuni kuma Cibiyar Maxar Technologies ta wallafa sun nuna sabbin ramuka da gine-ginen da aka lalata waɗanda ba a gan su ba bayan hare-haren Amurka
Ana iya ganin wani sabon rami a ɗaya daga cikin titunan zuwa wata mashigar hanyar ƙarƙashin ƙasa na cibiyar wadda ke arewa maso yamma
Sannan kuma ana iya ganin aƙalla ramuka guda biyu a kusa da wata hanyar ƙarƙashin ƙasa a gefen kudancin cibiyar
Hotunan Maxar sun kuma nuna wata tasha da aka lalata a arewacin cibiyar, tare da ramukan da hare-hare ta sama suka haddasa, ga kuma burbuɗin ƙara a dai wannan yankin
Ana kuma iya ganin ƙarin wani sabon rami da kuma alamun ƙonewa a tsakiyar wani titi a gefen yamma na cibiyar
An yi imani an kai hare-haren ne da nufin sanya zuwa cibiyar da gyara ta, su zama da matuƙar wahala
Tarin farar ƙurar da ake iya gani a wasu hotunan tauraron ɗan'adam mai yiwuwa alama ce ta girman ɓarnar da aka yi a can cikin ƙarƙashin ƙasa, kamar yadda masharhanta suka yi imani
"Ƙarfin fashewa a can cikin ƙarƙashin ƙasa ta haddasa tarwatsewar kankare kamar yadda aka bayyana, abin da zai iya janyo gagarumar ɓarna ga gine-ginen ƙarƙashin ƙasa," in ji Trevor Lawrence, shugaban Cibiyar Fasahar Makamashi a Jami'ar Cranfield kuma ƙwararre a kan illar da fashewar bam kan haifar
"La'akari da sarƙaƙiyar fasalin waɗannan gine-gine, gagarumar ɓarna idan ta faru, ba abu ne da mai yiwuwa za a iya gyarawa ba cikin taƙaitaccen lokaci."
Cibiyar Fasahar Sarrafa Nukiliya ta Isfahan da ke kudu maso gabashin Isfahan ita ce tashar binciken makamashin nukiliya mafi girma ta Iran
Tana kuma ƙunshe da tashar tace makamashin yuraniyam da ke gyara makamashin daga siffarsa ta asali a mayar da shi zuwa wani abu da za a iya ingantawa a cibiyoyin sarrafa makamashin ƙasar biyu na Natanz da Fordo
Kafin kuma Amurka ta jefa bama-baman tarwatsa gine-ginen ƙarƙashin ƙasa ranar 22 ga watan Yuni, lamarin da ya haddasa ƙarin gagarumin lahani a faɗin cibiyar
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya kare ingancin hare-haren da Amurka ta kai wa Iran, ga alama kuma yana bayani ne a kan cibiyar tace yuraniyam ta Isfahan
"Ba za ka iya yin makamin nukiliya ba idan babu cibiyar tace yuraniyam, har yanzu ba mu iya gano inda take ba, da inda take can baya a kan taswira - saboda gaba ɗaya komai ya koma baƙi ƙirin kawai
babu ita....ta shafe daga banƙasa."
An ɗauki hotunan gaba ɗayan cibiyar a na'urorin tauraron ɗan'adam na Maxar kuma an yi gagarumar ɓarna a ɗumbin gine-ginenta
Ɗaya daga cikin gine-gine, wanda a baya ake bayyana sunansa da Cibiyar Harkokin Kimiyya da Tsaron Ƙasashen Duniya kuma babban ginin tace yuraniyam, an yi masa raga-raga
Ana kuma iya ganin ƙarin ɓarna a ƙarin hanyoyin shiga na ƙarƙashin ƙasa a wani hoto
Ƙwararru daga kamfanin nazarin bayanan leƙen asiri na Maiar sun ƙididdige cewa mai yiwuwa ne hanyoyin shigar sun fuskanci "matsakaicin" lahani a gininsu
Sun lura da ƙonewa a gefen mashigun amma kuma ba su ga wata ɓarna a jikin kankaren da ke kusa ba, sannan kuma ba a ga ruftawar ƙasa a saman mashigun ba
Ƙoƙarin baya da Iran ta yi na ƙarfafa mashigar cibiyoyin ta hanyar jibge tarin ƙasa mai yiwuwa ya rage tasirin hare-haren na Amurka
"An ga wata hanyar ƙarƙashin ƙasa a cibiyar Isfahan kamar ta fuskanci fashewar wani abu daga ciki da kuma gobara, la'akari da baƙaƙen ɓaraguzai da suka tarwatsu a wajen hanyar
Idan ko haka ne, sai an kwashe shekaru kafin a iya gyarawa," a cewar Mark Cancian, daga Cibiyar Tsare-tsare da Nazarin Harkokin Ƙasashen Duniya
"A ɓangare ɗaya, kwaranyewar launi a jikin ginin mai yiwuwa ya faru ne sanadin fashewar makamin shi kansa amma ba saboda ratsawar makamin zuwa cikin ginin ba
Ɗaya hanyar shigar ita ma an ga kamar yashi da ƙasa duk sun turbuɗe ta
Idan haka ne kuwa, ana iya buɗe ta a cikin 'yan makonni."
A lokacin yaƙin Isra'ila da Amurka duk sun kai hare-hare kan Natanz, tashar sarrafa makamashin yuraniyam ɗin Iran ta farko
Hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar 22 ga watan Yuni, jim kaɗan bayan hare-haren Amurka sun nuna ramuka guda biyu a wani makeken yanki na tashar nukiliyar
An yi imani ramukan suna saman gine-ginen ƙarƙashin ƙasa da ke ƙunshe da zaurukan da na'urar makamashin nukiliya take, mai tace makamashin yuraniyam
Wani sabon hoto, da aka ɗauka ranar 24 ga watan Yuni, ya nuna ramukan da tuni aka rufe da ƙasa, waɗanda mai yiwuwa ke nuna ana ci gaba da aiki don gyara ɓarnar da aka yi wa tashar
"Yi tunanin abin da za ka yi mana idan rufin gidanka ne ya huje," in ji David Albright, " kuma mai yiwuwa suna so aƙalla su kafa wata garkuwa ga wani bam mai ratsa ƙarƙashin ƙasa da za a iya sake harbo shi wurin."
Wani muhimmin wuri da Isra'ila ta kai wa hare-hare a lokacin yaƙin shi ne filin jirgin sama na Mehrabad, a yamma da birnin Tehran
Filin jirgin da ya taɓa zama na zirga-zirgar ƙasashen duniya, yanzu mafi yawa yana karɓar jiragen sama masu jigila a cikin gida ne kawai
Isra'ila ta raba hotunan filin jirgin tana kai farmaki kan wasu jiragen yaƙin F-14 ƙirar Tomcat, waɗanda basaraken ƙasar Shah ya saya kafin juyin juya halin Musulunci na 1979
Wani hoto ma da aka ɗauka a shiyyar masana'antu a kudu da titin tashin jirgin, ya nuna ɓarnar da aka yi wa gine-gine birjik
Wani hoto kuma ya nuna wani sashe a yamma da titin saukar jirgi, inda aka ga aƙalla wani gidan ajiyar kaya gaba ɗaya an lalata
Sashen na ƙunshe da kamfanonin harkokin sararin samaniya da dama masu alaƙa da masana'antun tsaron Iran
Isra'ila ta zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, awanni bayan amincewa da yarjejeniyar wadda shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta
Ministan tsaro na Isra'ila, Israel Katz ya ce dakarun Isra'ila za su "mayar da mummunan martani kan karya yarjejeniyar" ta hanyar kai "munanan hare-hare" kan Tehran
Iran ta musanta cewa ta harba makamai masu linzami kan Isra'ila kuma dakarun ƙasar sun lashi takobin mayar da martani matuƙar Isra'ila ta ƙara kai musu hari
Ga wasu abubuwa da muka sani kan yarjejeniyar ya zuwa yanzu
Kimanin ƙarfe 5 na asubahin ranar Talata (agogon GMT) ne shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da sanarwar cewa yarjejeniyar ta fara aiki
"Don Allah kada a karya ta" kamar yadda ya buƙata daga ɓangarorin biyu a shafinsa na sada zumunta na Truth
Kimanin ƙarfe shida kuma na safiya (agogon GMT) Isra'ila ta tabbatar da cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar, bayan Iran ta nuna aniyar daina kai farmaki idan ita ma Isra'ila ta daina
Sai dai sa'o'i bayan haka ne Isra'ila ta zargi Iran da ƙaddamar da hare-hare a cikin ƙasarta
Tun farko Donald Trump ya ce "(sun) amince baki ɗaya" a wani bayani da ya wallafa jim kaɗan bayan ƙarfe 10 na dare a ranar Litini, wanda ya ce an kawo ƙarshen abin da ya kira "yaƙin kwana 12"
Hakan na zuwa ne bayan Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar a ranar Litinin, wani mataki da ta bayyana a matsayin ramuwar-gayya kan harin da Amurka ta kai a cibiyoyinta na nukiliya
Isra'ila ta zargi Iran da ƙaddamar da hari a cikin kasarta bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar Talata
Kafin fara aikin yarjejeniyar Iran da Isra'ila sun yi ta kai wa juna munanan hare-hare
Rundunar Sojin Isra'ila (IDF) ta ce makamai masu linzami na Iran da dama ne suka fada cikinta a daren Talata
Masu aikin ceto sun ce hare-haren sun kashe mutum huɗu da rauna wasu mutum 22 a garin Beersheba
A lokacin ne kafar talabijin ta gwamnatin Iran ta ce ƙasar ta harba "kashi na ƙarshe na makamai masu linzami" a kan Isra'ila
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta lalata cibiyoyin harba makamai masu linzami a yammacin Iran, inda suka ce an riga an ɗana makaman domin harbawa zuwa cikin ƙasarta
Iran ta ce an ƙara kashe wani masani kan nukiliya jim kadan kafin yarjejeniyar ta fara aiki
Babu tabbas kan adadin mutanen da aka kashe tun bayan ɓarkewar rikicin
Kafar yaɗa talabijin ta Iran IRINN ta sanar da cewa an tsagaita wuta tana mai cewa an tilasta wa Isra'ila bayan nasarar harin da Iran ta kai sansanin soji a Qatar
A sanarwar da kafar ta karanta a ta ce Trump ne ya roƙi a tsagaita wuta bayan harin na Iran
Sannan sanarwar ta yi jinjina ga dakarun juyin juya hali na Iran
Ministan harakokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na X cewa Iran ta ci gaba da kai wa Isra'ila hari har zuwa karfe huɗu na safe
Ya ce ƙarfe huɗu na safe ne wa'adin da aka ba Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare
A cewarsa "idan har Isra'ila ta yi haka, to ba mu da niyyar ci gaba da kai hare-hare
Isra'ila har yanzu ba ta ce komi ba game da tsagaita wutar da Trump ya sanar, kuma ko bayan sanarwar Trump ta kai hare-hare ta sama cikin Iran
Da safiyar Talata ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran ta fara aiki
Sai dai shugaban ya yi kira ga bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar
Donald Trump ya sanar da tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Iran a ranar Litinin da dare a shafinsa na sada zumunta
Trump ya ce Iran za ta fara aiwatar da tsagaita wutar, daga baya kuma Isra'ila za ta dakatar da kai wa Iran hari
Isra'ila dai ta ci gaba da kai hare-hare cikin Iran, kamar yadda ministan tsaronta ya bayyana, yayin da kuma Iran ta yi gargaɗi ga mazauna birnin Ramat Gan kusa da Tel Aviv su fice
Shugaban na Amurka ya ce tsagaita wutar za ta fara aiki "nan da awa shida" tare da cewa nan da sa'a 24 "za a kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran
Sai dai Isra'ila da Iran ba su tabbatar da cewa sun tsagaita wuta ba
Babu tabbas ko rikicin tsakanin ɓangarorin biyu zai kawo ƙarshe, ko tsagaita wutar da Trump ya sanar za ta tabbata
Shugaban Amurka ya kira sabon rikicin na Isra'ila da Iran da sunan "yaƙin kwana 12."
"Wannan yaƙi ne da za a iya shafe shekaru ana yi, wanda zai iya tarwatsa yankin gabas ta tsakiya, amma hakan ba ta faru ba, kuma ba za ta faru ba," kamar yadda Trump ya bayyana a shafinsa na sada zumunta
Abu ne da yake a bayyane cewa Isra'ila ta mallaki makaman nukiliya tun shekarun 1960
To amma kuma duk da haka ba ta taba fitowa fili a hukumance ta tabbatar tana da su ba
"Isra'ila ce kasa daya kawai a Gabas ta Tsakiya da ke da makaman nukiliya," in ji Javier Buhigas, masani a kan ilimin sifa (physics) kuma mai bincike a cibiyar nazarin zaman lafiya ta Dallas - da ke nazari kan zaman lafiya da tsaro da makamai
Ita kuwa Iran kamar yadda hukumar nukiliya ta duniya ta tabbatar ta inganta sinadarin yuraniyom har zuwa kashi 60 cikin dari
Ita dai Isra'ila ba ta taɓa sanya hannu kan yarjejeniyar hana bazuwar makaman nukiliya ba , yayin da kasasahe irin su Iran da Amurka da Rasha su kuwa sun amince da wannan yarjejeniya
Wannan na nufin cewa Isra'ila ba kamar sauran kasashe mambobin hukumar nukiliya ta duniya ba (IAEA), ba za a riƙa kai mata ziyara a cibiyoyinta da ake ganin na nukiliya ne ba
Bisa wadannan dalilai duk wani bayani da ake da shi a kan shirin nukiliya na Isra'ila, yawanci an same shi ne ta hanyar satar fitar da bayanai da rahotanni daga ma'aikatar tsaro ta Amurka da ma'aikatar makamashi da kuma kiyasin hukumomin duniya da ke sanya ido kan batutuwan nukiliya
Akwai kuma bayanan da aka samu daga Mordechai Vanunu, wanda injiniya ne na nukiliya na Isra'ila, wanda ya yi aiki a daya daga cikin cibiyoyinta na nukiliya, wanda bayan an kore shi daga aiki ya yi hira da jaridar The Sunday Times a 1986
Shi ne mutum na farko da ya fara tona asiri cewa Isra'ila tana da cikakken shirin nukiliya, kuma wannan tonon silili da ya yi ne ya sa aka daure shi a gidan yari tsawon shekaru
A hukumance ita Isra'ila tana da wata manufa da take kira ''Amimut'', ta barin harkokinta na nukiliya a dukunkune - wato ita ba ta fio fili ta ce tana da nukiliya ba kuma ba ta fito ta karyata cewa tana nukiliya ba
Kuma wannan manufa ba wata sabuwa ba ce an san ta daman kamar yadda Avner Cohen farfesa nazari a kan hana bazuwar makaman nukiliya - kuma kwararre a kan shirin nukiliya na Isra'ila ya rubuta a wani rahoto ga Majalisar Magabata ta Birtaniya (British House of Lords)
Ita wannan manufa tana da wani tasiri kamar yadda Shimon Pere - tsohon Firaminista kuma tsohon Shugaban Kasar Isra'ila, ya rubuta a littafin tarihinsa:
"Mun fahimci cewa barin abu a dukunkune yana da matukar tasiri
Rashin tabbas ko tantama gargadi ne mai karfen gaske da zai tsoratar da duk wani da zai sake tunanin yi wa Yahudawa kisan-kiyashi na biyu (Holocaust)."
Cohen ya ce wannan manufa ta barin shirinta na nukiliya a dukunkune ga duniya, ita ce babbar dabarart da kuma nasara a fannin diflomasiyya
Masanin ya ce wannan manufa tare da shiru da kasashen duniya suka yi, hakan ya ba Isra'ila damar cin moriyar yanayin biyu - na cewa tana da makaman nukiliya da kuma na cewa a'a ba ta da makaman nukiliya - wanda hakan ya kare da daga binciken hukumar hana bazuwar makaman, tun da ita ba mamba ba ce kuma dadin-dadawa ba ta fito ta ce tana da makaman ba
End of preview. Expand in Data Studio

Dataset Card for "bbc_dataset-2"

More Information needed

Downloads last month
0