text
stringlengths 20
374
|
---|
Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa za a cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba za a aika masu kowane irin bayani kan masu shiga gasar ba |
Tawagar alƙalan za ta zaɓi labarai 30 bayan tantancewa ta farko sannan daga bisani za a sake tantancewa a fitar da guda 15, inda a tantancewa ta uku za a fitar da ta ɗaya da ta biyu da ta uku sai kuma 12 da suka cancanci yabo |
Waɗanda suka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan ɗaya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu ɗari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu ɗari biyar) ga wadda ta zo ta uku |
Za a sanar da mutum ukun da suka zamo zakaru a yayin wani bikin karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya |
Shagalin bikin mawaƙi Dauda Kahutu da amaryarsa Aishatu Humaira na cigaba da jan hankali, inda ake cigaba da tattaunawa kan bikin a kafofin sadarwa musamman bayan shagalin cin abincin dare na bikin da aka yi a jihar Kano |
Abubuwan da suka ɗauki hankali sun haɗa da adon da amarya da ango suka sha, kwalliyar da aka yi a zauren walima da kuma manyan baƙin da suka halarci daurin auren da kuma walima |
Biki ne da aka yi na ƙasaita musamman ganin yadda mawaƙi Rarara ke jan zarensa a wannan lokaci har ma wasu ke kwatanta shi da shahararrun mawaƙan ƙasar Hausa da suka gabata, sanadiyyar baje-kolin basirar da yake yi a cikin waƙoƙinsa |
Ba wannan ne karon farko da jaruman masana'antar suke yin shagalin biki na ƙasaita, wanda ke ɗaukar hankalin mutane ba |
A ranar Juma'a, 25 ga watan Afrilun shekarar 2025 ce aka ɗaura auren Dauda Kahutu Rarara da amaryarsa Aisha Ahmad wadda aka fi sani da Aisha Humaira a garin Maiduguri na jihar Borno |
An daɗe ana rade-raɗin akwai soyayya tsakanin ma'auratan biyu, amma a duk lokacin da aka tambaye su, sai su ce aiki ne kawai |
A shekarar da ta gabata mawaƙin ya rera waƙar 'Aisha', wadda a ciki ya baza kalaman soyayya har aka yi ta cewa da ita yake yi |
Amma sai aka yi amfani da waƙar a fim ɗin jarumar mai suna 'A cikin biyu' wanda Ali Nuhu ya hau |
Dauda Kahutu Rarara fitaccen mawaƙi ne da ya daɗe yana jan zarensa, musamman a waƙoƙin siyasa, kafin daga baya ya fara rikiɗewa zuwa kafofin soyayya da wayar da kan mutane |
Masoyansa na masa kallon mawaƙin da ya fi tashe a wannan zamanin, musamman ganin yadda waƙoƙinsa suke jan hankalin mutane a duk lokacin da ya fitar da sabuwa |
Daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren akwai jiga-jigan ƴansiyasa irin su tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da Mataimakin shugaban majalisar Dattawa ta Najeriya Sanata Barau Jibrin da sauransu |
Abubakar Bashir Maishadda mai shirya finafinai ne a masana'antar Kannywood wanda ake wa laƙabi da 'king of box office' saboda yadda finafinansa suka fi samar da kuɗi a sinima |
Furodusan ya aure jaruma Hassana Muhammad ne, wadda ta ja wasu finafinan kamfaninsa, ciki har da Hauwa Kulu da sauransu |
An ɗaura aurensu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris na shekarar 2022 a Masallacin Murtala da ke jihar Kano |
Maishadda ya yi aure ne a lokacin da finafinansa suke tashe a masana'antar, inda yake fitar da finafinai manya tare da jarumai mata masu tashe |
Hakan ya sa aka riƙa alaƙanta shi da jarumai mata da yawa da suke fitowa a finafinansa |
Daga cikin waɗanda aka riƙa alaƙanta shi da su akwai jaruma Maryam Yahaya, kafin daga baya ya sanar da aurensa da Hassana |
Ɗaya daga cikin bikin ƴan Kannywood da za a daɗe ba a manta da shi ba shi ne na taurari biyu da suke tashe a lokacin da suka yi aure, wato Sani Musa Danja da Mansurah Isah |
A ranar 14 ga Yuli na shekarar 2007 ce aka yi bikin auren jaruman, inda aka gudanar da biki na kece-raini da ƙasaita |
Sani Danja ya yi tashe da farin jini wurin ƴanmata inda aka riƙa alaƙanta shi da taurari mata daban-daban, ɗaya daga ciki da ta yi fice ita ce Maryam Jan kunne, amma daga bisani ya rufe kunnensa ya zaɓi Mansurah Isah |
Sani Danja da Mansurah suna cikin ƴan fim na farko-farko da suka auri juna, kuma suka daɗe suna tare kafin auren ya mutu |
Allah ya albarkaci auren da ƴaƴa huɗu: Iman da Khalifa da Sultan sai kuma ɗan autansu Sudais |
Wani auren da ya janyo taƙaddama da muhawara a shafukan sada zumunta shi ne na Ummi Rahab da Lilin Baba |
Ummi ta taso cikin masana'antar Kannywood a matsayin ta hannun damar babban tauraro Adam A |
Zango, tun daga fim ɗin da ta fara fitowa wato 'Ummi' |
A lokacin da auren ya taso an yi ta raɗe-raɗin cewa Zango ya yi adawa da auren, sai dai duk da haka an ɗaura auren kuma Ummi da Lilin Baba na ci gaba da zamansu a matsayin mata da miji |
Yayin da wasu ke zargin Ummi Rahab da juya wa wanda ya raine ta a masana'antar baya, wasu kuma sun zargi Zango da ƙoƙarin hana matashiyar rawar gaban hantsi |
An ɗaura auren Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar Asabar 18 ga watan Yulin shekarar 2022 a Tudun Murtala da ke jihar Kano |
Waɗanda suka daɗe suna bibiyar harkokin fim ɗin Hausa sun san irin tashen da Fati Muhammad ta yi, a matsayin ɗaya daga cikin taurari mata na farko-farko da suka haska a masana'antar Kannywood |
Wasu na ganin cewa ya zuwa wannan lokaci babu tauraruwar da ta shiga zukatan masu kallo kamar yadda Fati Muhammad ta yi a lokacin da take zamaninta |
Auren jarumar da Sani Mai Iska ya bai wa mutane da dama mamaki kasancewar an fi alaƙanta ta da wasu fitattun taurari maza |
Ɗaya daga cikin waɗanda aka riƙa alaƙanta ta da su shi ne babban tauraro Ali Nuhu, bayan rawar da suka taka tare a fina-finai da dama, kamar irin su Sangaya da Mujadala |
Aurenta da Sani Mai Iska ya cigaba da jan hankali musamman ganin yadda suka bar ƙasar zuwa Birtaniya bayan auren |
Sai dai auren ya mutu daga baya, duk da cewa har yanzu ba a san takamaiman abin da ya raba su ba, duk da cewa akwai raɗe-raɗi da dama da ake yaɗawa, amma sun daɗe suna musantawa tare da cewa akwai aminci a tsakaninsu |
Ɗaya daga cikin auren da masu kallo suka fi yin na'am da shi a tarihin masana'antar Kannywood shi ne na Ahmed S |
Nuhu da Hafsat Shehu |
Mutanen biyu sun kasance abin so ga mutane da dama da ke kallon fina-finan Hausa na wancan lokacin |
Hakan bai rasa nasaba da shaidar da aka yi wa Ahmed na kasancewa mai son zaman lafiya ba duk da rikice-rikicen da ake fama da su a masana'antar |
A bangare ɗaya Hafsat kan fito a yawancin fina-finai a matsayin mai sanyin zuciya da fara'a, lamarin da ya sa take burge masu kallo |
Tauraruwar ta fara tashe ne bayan fim ɗinta na Zabari na kamfanin FKD, wanda daga lokacin soyayya ta ƙullu har ta kai ga aure |
Sai dai auren bai daɗe ba, kasancewar ya rasu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota a garin Azare na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya |
Fim ɗin Lerawa Production da ake kira Wasila, shi ne fito da Wasila Isma'il a duniyar fim na ƙasar Hausa |
Aurenta da Al'amin Ciroma ya ja hankali sosai, duk da cewa a lokacin ba a samu yalwatuwar kafofin sada zumunta irin yanzu ba |
Auren ya ɗauki hankali ne saboda ya zo a daidai lokacin da masu kallon finafinan Hausa suke cigaba da tattaunawa game da fim ɗin 'Wasila' |
Wasila Isma'il wadda ta fito a matsayin matar Ali Nuhu cikin fim ɗin 'Wasila' bayan tafka soyayya mai ratsa zukata, ta jefa masu kallo cikin jimami bayan cin amanar Jamilu da wani tsohon abokinta mai suna Moɗa |
Soyayyar Wasila da Jamilu na daga cikin soyayya mafi zafi da aka taɓa gani a duniyar fina-finan Hausa |
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta tabbatar da bin haƙƙin mutanen jiharta matafiya da aka kashe a jihar Filato a ranar Asabar |
Mutum 12 aka kashe ƴan asalin jihar Kaduna a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato yayin da suke kan hanyar zuwa ɗaurin auren ɗan'uwansu cikin motar bas mallakin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria |
Gwamnatin Kaduna ta ce mutum 16 ke kwance a asibiti da aka jikkata a harin na Mangu daga cikin mutum 31 da ke cikin motar matafiyan |
"Na kira gwamnan Filato kuma na nuna masa rashin jin daɗinmu kan wannan hali da aka yi na rashin hankali kuma ba za mu bari ya tafi a haka ba," in ji Gwamna Uba Sani |
Gwamnan ya kuma ce ya tattauna da shugaba Bola Ahmed Tinubu game da al'amarin da kuma babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro Malam Nuhu Ribadu |
Ya ce irin yadda ake kashe mutane a jihar Filato ba za a bari ba idan har gwamnati ba ta ɗauki mataki ba |
A cewar gwamnan, babu wani dalili da mutanen da ba su ji ba su gani ba suna kan hanya a tare su a kashe |
"Na faɗa wa gwamnan Filato cewa dole ne a ɗauki mataki domin ba za a mayar da jiha ba ta koma ta kashe mutane kawai." |
"Na faɗa wa gwamnan cewa abin da ake yi a Filato dole a bari, idan kuma ba a bari ba to laifin gwamna ne," in ji shi |
Sai dai gwamna Uba Sani ya ce, gwamnan Filato ya tabbatar masa da cewa an kama mutum 22 da ake zargi suna da hannu a kisan matafiyan na jihar Kaduna a Mangu |
Amma gwamnan na Kaduna ya ce duk da an kama su dole a faɗaɗa bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu da aikata kisan a kuma hukunta su |
"Na faɗa wa shugaban ƙasa cewa zan bi diddigi a matsayina na gwamnan jihar Kaduna domin tabbatar da cewa an ɗauki mataki daidai da laifin da suka yi na kisa," in ji Gwamna Uba Sani |
Gwamnan ya ce zai tsaya tsayin daka domin tabbatar da an kawo karshen matsalar kashe-kashe a jihar ta Filato |
Tuni shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi allawadai da harin na Filato, jihar da ta daɗe tana fama da rikicin na ƙabilanci da addini da kuma na makiyaya da manoma |
Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNCPL ya sanar da ƙarin farashin man fetur a gidajen mansa da ke faɗin ƙasar |
Kamfanin ya ƙara farashin zuwa naira 945 a gidajen mansa da ke Abuja, yayin da sabon farashin a legas yake naira 915 |
Ƙarin na NNPCL na zuwa ne ƴan kwanakin bayan matatar mai ta Dangote mai zaman kanta a ƙasar ta sanar da ƙarin farashin a depo zuwa naira 880 kowace lita |
Ƙarin farashin ba ya rasa nasaba ta tashin man a kasuwannin duniya da aka samu sakamakon yaƙin Isra'ila da Iran |
Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin ƙasashen biyu na ci gaba da haifar da tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya |
A jiya Litinin an sayar da gangar ɗanyen man fetur kan dala 80, sakamakon ƙaruwar tashin hankalin, bayan shigar Amurka cikin yaƙin |
Iran na cikin manyan ƙasashen duniya masu arzikin man fetur, da ke fitar da shi zuwa kasuwannin duniya, kamar yadda Datka Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur a Jami'ar Nile da ke Abuja ya bayyana |
'Iran ce ƙasa ta biyar a jerin ƙasashen duniya masu arzikin man fetur, inda take fitar da ganga kimanin miliyan huɗu a kowace rana'', in ji shi |
Ya ƙara da cewa ƙasar na daga cikin jerin ƙasashen da suka fi samar da man fetur mai araha a duniya |
Tuni shugaban Amurk, Donald Trump ya yi kira da a sauko da farashin man a kasuwannin duniya |
Injiya Yabagi Sani mai Sharhi kan al'amuran man fetur a Najeriya ya ce abin da ya shafi sauran ƙasashen duniya shi ne ya shafi Najeriya |
''Abin da ke faruwa shi ne kusan kashi 20 zuwa 30 na man fetur da ake hada-hadarsa a kasuwannin duniya ana yi ne ta mashigar Hormuz, wanda ke ƙarƙashin ikon Iran'', |
Ya ƙara da cewa sakamakon yaƙin, Iran ta yi barazanar rufe mashigin, kuma saboda fargabar abin da ke je ya zo tuni jiragen dakon man fetur suka fara kauce wa mashigar, lamarin da ke haifar da ƙarancin man a kasuwannin duniya |
Dakta Ahmed Adamu ya ce galibi man fetur da ake amfani da shi a Najeriya, ana shigar da shi ne daga ƙetare |
''Kuma ita kasuwar man fetur galibi a dunƙule take, idan aka samu tashin man a kasuwar duniya dole a same shi a ko'ina, ciki har da Najeriya'', in ji shi |
Injiniya Yabagi Sani ya ce ''Idan ka ɗauki matatar mai ta Dangote wadda ita ce ke samar da mafi yawan mai da ake amfani da shi a Najeriya, tana shigo da ɗanyen mai ne daga waje, to ka ga idan ta sayo da tsada, ai dole ya sayar da tsada'', in ji shi |
Ya ƙara da cewa shi kansa babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL yana shigo da mai daga ƙetare |
Masanin man fetur ɗin ya yi gargaɗin cewa ba ma kaɗai man fetur ba, farashin komai zai iya tashi a cikin ƙasar, sakamakon wannan yanayi da aka shiga |
''Saboda idan ka duba ita wannan mashiga ta Hormuz ba man fetur kaɗai ake hada-hada ta ciki ba har da na abinci da sauran abubuwa, kuma ka san indai farashin mai ya tashi a Najeriya to yana shafar kusan komai a cikin ƙasar'', in ji shi |
Injiniya Yabagi Sani ya ce gwamnatin Najeriya za ta amfana da wannan ƙarin mai da aka samu akasuwannin duniya |
''Saboda za ta samu ƙarin kuɗin shiga, tattalin arzikinta zai bunƙasa'', kamar yadda ya bayyana |
Ya ci gaba da cewa ''gwamnatin Najeriya ta ƙayyade kasafin kuɗinta kan farashin dala 75 kan kowace gaggar mai, to idan aka samu ƙari, kwanan gwamnati za ta samu rara na abin da ta ƙayyade za ta kashe a shekarar da muke ciki'', in ji shi |
''Hakan zai sa a samu ƙaruwar ayyukan ci gaba a cikin ƙasa, da samar da ayyukan yi ga ƴan ƙasar, sakamakon ƙarin kuɗin shiga da gwamnati ta samu'', in ji shi |
To sai dai Dakta Ahmed Adamu ya ce duk da ƙarin kuɗin shiga da gwamnatin Najeriya za ta samu sakamakon tashin farashin man fetur ɗin, akwai hatsarin samun tashin farashin kayyaki da tsadar rayuwa a Najeriya |
''Idan aka samu tashin farashin mai, to su ma gidajen mai za su ƙara farashin mai, don haka farashin komai zai ƙara a ƙasar, sakamakon ƙaruwar kuɗin sufuri.'' in ji shi |
Abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta inganta ayyukan matatun man fetur huɗu da take da su domin tallafa wa ƴan ƙasar, a cewar Injiniya Yabagi Sani |
''Kuma tunda matatun na gwamnati ne, gwamnati za ta iya rage farashin da za ta sayar wa masu gidajen mai a ƙasar domin tallafa wa ƴan ƙasar'', in ji shi |
''Ai dama ƙarƙashin dokokin Najeriya akwai wani adadi na man fetur da aka ware domin ƴan ƙasar su yi amfani a cikin Najeriya'', in ji shi |
Injiya Yabagi Sani ya ce ita matatar mai ta Ɗangote tun da ta ɗan kasuwa ne mai zaman kanta, ba za ta iya rage farashin man ba, tun da sayowa ta yi |
To amma ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta ci gaba da amfani da tsohon tsarin sayar wa matatar ɗanyen man da ka haƙo a cikin ƙasar, ta hanyar amfani da naira |
''Haƙiƙa wannan zai taimaka wajen rage farashin man a cikin ƙasa, saboda Dangote ya saya da araha, don haka shi ma zai sayar da araha'', in ji shi |
To sai dai Dakta Ahmed Adamu ya ce a irin wannan yanayi, babu abin da gwamnatin Najeriya za ta iya yi, saboda a tuni gwamnati ta fitar da hannunta a cinikayyar man fetur bayan janye tallafi |
''Gwamnatin Najeriya ta riga ta bar kasuwancin mai a hannun kasuwa, wato kasuwa ta yi halinta, kuma dama ita kasuwa ta gaji riba da faɗuwa'', in ji shi |
Lokutan su ne: 0530,0630,1400,1930 GMT |
Sannan akan kama waɗannan shirye-shirye a gidan Radio Anfani a kan zango 100Mhz a Damagaram da Maraɗi |
Rana takan shiga wani yanayi na yawaitar tunzuri inda takan yi amon wuta, wanda a bana ya kai ƙololuwa, kamar yada hotunan da hukumar lura da sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta fitar suka nuna |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.