text
stringlengths 2
189
|
---|
Magaji ne yake karatu a sashen lafiya. |
Ali ya yi amfani da tsohuwar hanyar bikin haihuwa. |
An fi samun gizo gizzo a gidan da ba jama'a. |
Akwai shirin da zan ji a rediyo anjima. |
Kakata ta bamu labarin wata barewa. |
A jirgi na je Madina. |
Na ce ka daina irge zuwa ɗari biyar? |
Konuwar sa zata warke nan da kwana biyar |
Shuɗi mai hasken kayan da hafsan ɗan sandan da ya saka shima yana daga cikin kayan ƴan sanda. |
Yaran suna yar tsere da karnukan. |
Daya daga cikin ma'aikaciyar otel din za ta je ta canza zanin gadon dakin da na zaba. |
jami'a na da kansila |
A ina aka musu kaciya? |
Zabarta na asoebi ya burge ni. |
Baza ka buga wasan ƙwallon ba. |
Shin masu zuwa za su fuskanci wani sabon ƙalubale tare da haɓakar rigunan hidima a Kano? |
Wai matuƙan jirgin suna barci lokacin da suka tuka jirgin? |
Ladi ta ɗaura zani da riga |
Gandirebobi ma suna da nasu yinifom. |
Zaki na iya kashe mutum. |
Ana iya sauraren labarai a tashar rediyo. |
Babu gidaje da yawa a unguwar mu. |
Wasop, na da saurin tura saƙo |
Sabon injiniyan kenan. |
Wasu guduman na da nauyi. |
Talatu zata koma sabon gida |
Mama ina da gwajin makaranta shiyasa ban gyara ta ba |
An watsar da al'adar yin tatsuniya. |
Alkali ya tura matasa kurkuku zaman jiran shari'a |
Mace mai alheri tana da girma. |
goggon tamu kwata kwata ta tsane mu saboda mahaifiyar mu |
Kun je gidan wasan kwaikwayon? |
Malamin mu ya kira rajista da safe |
A a ba a saka ranar aurenta ba tukunna. |
Sanin gaibu sai Allah |
Jeka ofishin ku a yanzu |
Tsakiyan inganci shine take'n jihar Kaduna. |
Za a ba mu fasfo ɗin mu gobe. |
Kullum ina siya gala a shago. |
Yawancin yaran yau basu iya ƙirgan gargajiya ba |
Cokalin ya lankwashe |
Wanda ya shigar da karar da shaidarsa suna cikin tashar jirgin ruwa |
An canza sunan masallacin unguwar mu. |
Masu satar mutane suna zalintar waɗanda suka ɗauka. |
Kada ka siyo shinkafa! |
Babata tana gyara kantocin ɗakin girkin ta, yau. |
kakanmu ya ce bai je makaranta ba saboda rashin kuɗi |
Mun ƙirƙiro rajistar da zamu dinga sanya sunan duk sabon ɗan ƙungiya |
Farashin nama kilo ɗaya yanzu ɗari takwas da hamsin ne |
Masoyan sun gaya mun cewan a tashan mota na jabi suka fara magana shekara uku da ya wuce |
Stabiliser yana kara karfin kayan wuta a gida. |
A watan nan za'a gabatar da sabbin dabarbarun kitson Iko domin haɗa fasahar zamani da al'ada |
Kananan jariran kada sun ruga zuwa ruwa |
Yaran Jon sun tafi koyan Baibil. |
Magungunan zasu fara aiki gobe. |
Yawancin mutane suna cin zarafin magungunan da ake ba su daga asibiti |
Menene sinadarin meat pie? |
Ana samun riɓa a harkar shirin film. |
Manoma na da hanyoyi da dama na noma. |
Aa ban samu na siya simintin ba. |
Datti ya ce mafi yawanci almajirai ne suke yin wasan damben gargajiya |
Taimakon motsin rai yana da mahimmanci yayin kalubale |
Likita na rubutawa marar lafiya yadda zai sha magani. |
Ina da murjani da kaka ta ta bani. |
Cizon cinnaka yana da zafi |
Shin ka bata zobon ne? |
Kin taka daga makaranta ne? |
Ka je aiki ranar laraba da ta wuce? |
Bob Marley Dan kasar Jamaika ne mai salon wakan rege. |
Cutar korona ta kashe mutane da yawa. |
Kwana bakwai ne a cikin sati. |
Ni da abokai na zamu ɗan hadu wannan asabar ɗin. |
Wuƙar sassaƙar tana cikin adakar gefe |
ɗakin aladen na ta wari da muka wuce . |
A'a, ƙusa bai cake ƙafana ba. |
Ya kai yaron shi ya je koyon aikin kafinta. |
Wani Cheetah yana bin mu kuna tambayata ko namiji ne ko mace |
Ruwan zamzam ruwa ne daga Allah |
Ba wanda zai je ofishin shedimasta sai da safe |
Na gan fuskan mutumin da ke dakin tsoro lokacin wasan nishadin,Mallam Danladi ne. |
Ina samun buhu kaman goma |
Kafiteriyar Silantiro daya ne daga cikin sannannun wajen abinci a Kano. |
Zo mu hadu bishiyar nan |
Ya ba su kyautar agogo ranar Lahadi. |
Na tsana naman Alaɗe amma sun ce za su sayo gobe |
eh ta yi gulma na |
Bayan dubu daya dari takwas da hamsin da shida sai dubu daya dari takwas da hamsin da bakwai. |
Ta haifi yara biyu. |
Aliyu zai shiga gudun bada sanda sati mai zuwa. |
Ilimin kimiyar noma shi ke samarwa duniya abinci. |
Akwai durowa a kowane ofis na ajiye takardu masu amfani. |
Baƙar allo fata abu ne da ake amfani da shi a makarantu don rubutu. |
Rikicin ƙasa da iyaka yana yawan faruwa a Katsina. |
Mota ya fi sauri tafiya fiye da keke. |
Abin ƙi ne mace ta samu ciki ba tare da aure ba. |
Zoben da musa ya siya ze kode nan da lokaci kadan |
Yakubu ya bar takalminsa a wajen bikin aure a makon jiya |
Akwai malamai a jami'a. |
Za ki shuka gwandan daji a gida ki? |
Wasu ƙasashen zasu ƙulla kasuwancin zoɓo da najeriya |
Subsets and Splits
No community queries yet
The top public SQL queries from the community will appear here once available.